Haɗin-kai shi ne zai kawo ƙarshen matsalar tsaro a Zamfara
A Jihar Zamfara akwai mutanen da suke so su jingina wannan matsala ga jami’an tsaro ko gwamnati.
Haɗin-kan shugabannin Jihar Zamfara tun daga Gwamna mai ci a yanzu da Minista a Ma’aikatar Tsaro wanda ɗan asalin jihar ne da tsofaffin gwamnoni da sanatocinmu da ‘yan majalisarmu na tarayya da na jiha tare da malaman addini da ‘yan kasuwa da sarakuna da duk masu faɗa-a-ji a Zamfara shi ne hanyar samar da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.
Al’ummar Jihar Zamfara matsayinsu na masu ilmi, waɗanda addinin Musulunci ya yi tasiri a kansu kuma mutane masu riƙo da gaskiya da mayar da alheri da alheri, ina amfani da wannan dama in bai wa junanmu shawara cikin mutuntawa da girmamawa ba tare da bayyana ra’ayi irin na siyasa ba.
- Zan dawo da martabar ilimi a Zamfara — Dauda Lawal
- Manoma sun koka kan yadda makiyaya ke cinye musu gonaki a Gombe
Ni ina ganin duk mutumin da yake kishin Jihar Zamfara da gaske ba kishi irin na siyasa ba, to akwai inda ya kamata ya ba da tasa gudunmawa a kan sha’anin tsaro a jihar ba ta hanyar sukar gwamnati ba, domin kuwa har abada cin zarafin gwamnati ba zai taɓa zama maslaha ga sha’anin tsaron jihar ba.
Al’ummar Zamfara, matsalar tsaron da wannan jiha ke fama da ita, jarrabawa ce daga Allah (SWT) abin ya wuce a yi wasa da hankali.
Mu daina yaudarar kanmu da abin da ba wannan ba, mu cire siyasa mu kalli abin da idon basira.
Kowane mutum a duniyar nan tara yake bai cika goma ba.
Mu yi wa gwamnati adalci; a cikin gwamnati akwai sanatoci da ’yan majalisa waɗanda suke da manyan kwamitoci. Idan har masoyanku ne ina suke? Wane irin hoɓɓasa suka yi game da sha’anin tsaron yankunanmu?
Al’ummar Zamfara, wallahi Allah (SWT) mai adalci ne kuma ba Ya zalunci sannan bai yarda mu yi zalunci ba.
A Jihar Zamfara akwai mutanen da suke so su jingina wannan matsala ga jami’an tsaro ko gwamnati, ya kamata su fito su bayyana wa duniya mutanen da ke da alhakin kashe al’ummar wannan jiha, tun da ba su yarda Allah ne Ya kawo wannan jarrabawa ba ko sai lokacin siyasa idan sun sake buƙatar ƙuri’unku?
Al’ummar Jihar Zamfara, mece ce ribar ƙarya da ƙage ko sharri a kan matsalar tsaron wannan jiha?
Wannan matsala ta kowa ce, duk wanda yake kishin jihar ina ganin ya kamata komai rashin ƙarfinsa akwai inda amfaninsa yake, sai ya ba da tasa gudunmawa gwargwado, amma ba mutum ya fake da matsalar tsaro, yana sukar gwamnati ba, bayan mutanen ƙauyuka a wannan jiha suna cikin musibar mahara.
Bayyana wa duniya gaskiyar halin da wannan jiha take ciki shi ne zai sa bayin Allah daga ko’ina a duniya su taimaka mana da addu’o’i ba ta hanyar rubutu a kafafen sadarwa ana cin zarafin gwamnati ba.
Matsalar tsaron nan, wallahi sai an cire siyasa da bambancin ra’ayi, sannan a yi wa kowa adalci, a tunkari matsalar tsaron gadan-gadan da gaske.
Sannan kuma al’umma kowa ya gyara tsakaninsa da Ubangijinsa a kuma bi shawarwarin dattawa masana tsaro, sai kuma a yi addu’o’i a masallatai da makarantun Islamiyya, idan ta kama a ɗauki malaman addinin Musulunci su tafi Kasa Mai tsarki domin roƙa wa jihar mafita sai a yi hakan.
Ya Allah Ka kawo wa al’ummar Jihar Zamfara ɗauki.
Ɗanƙane, shi ne Shugaban Kungiyar Arewa Media Writers na Jihar Zamfara.