Haɗurra 3 sun yi ajalin mutane 91 a kwanaki takwas — FRSC

Haɗarin da ya faru a Jihar Neja a ranar 8 ga watan Satumba, ya yi ajalin mutane 48.

Haɗurra 3 sun yi ajalin mutane 91 a kwanaki takwas — FRSC

Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) ta ce ta rayukan mutane 91 sun salwanta sanadiyyar wasu haɗurra uku da suka auku cikin kwanaki takwas a wannan wata na Satumba.

Shugaban Hukumar FRSC, Shehu Mohammed, ne ya sanar da hakan yana mai kokawa kan lamarin.

Da yake jawabi a wata hirarsa da manema labarai da kuma masu ruwa da tsaki a Abuja ranar Alhamis, ya ce haɗurran sun haɗa da wanda ya faru a Jihar Neja a ranar 8 ga watan Satumba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 48.

Ya kuma ce wani haɗarin da ya auku a Sabon Wuse a ranar 12 ga watan Satumba, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 18 tare da jikkatar mutane 18.

Haka kuma, ya ce wani haɗarin da ya auku a Jihar Kaduna a ranar 15 ga watan Satumba, ya yi sanadin mutuwar mutane 25.

A cewarsa, haɗarurrukan uku sun tabbatar da cewa sun auku ne babu makawa, ya

Ya ce a yayin da gwamnati ke iya ƙoƙarinta wajen samar da kayayyakin sufuri da kuma kula da harkokin sufuri kamar yadda aka tsara ko’ina a faɗin duniya, wasu matafiyan musamman direbobi sun ci gaba da yin watsi kan wannan ƙoƙarin

Ya koka da cewa duk da matakan da jami’an suka ɗauka ta hanyar tsarin kula da zirga-zirgar ababen hawa (RTSSS) da aka ƙaddamar domin magance matsalolin hanyoyin a ƙasar, akwai buƙatar ganawa da masu ruwa da tsaki.

Dangane da hakan ne Mohammed ya umurci kwamandojin rundunar da su tabbatar da an kiyaye doka da oda ba dare ba rana domin a samu sauƙin wannan lamari.

Ya ce, taron na da nufin magance ƙalubalen ƙa’idojin kiyaye hanyoyi da ake fuskanta a tituna da suka haɗa da ɗaukar abubuwa masu fashewa da ka iya haddasa gobara, tafiye-tafiye da daddare, gudun wuce ƙima da kuma illar da suke yi a kan manyan titunan ƙasar.

Ya ce yana fatan bayan taron, haɗurran tituna za su ragu matuƙa nan da ƙarshen shekara a yayin da yake kira ga buƙatar a haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen daƙile aukuwar rasa rayuka a manyan tituna.