Haaland ya kafa sabon tarihi a Firimiyar Ingila
A makon da ya gabata Haaland ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan UEFA na bana.
Dan wasan Manchester City, Erling Haaland, ya kafa tarihin zama dan wasan mai saurin taka rawa a cin kwallo 50 a babbar gasar tamaula ta Ingila.
A yanzu Haaland yana da hannu a kwallo 51, wanda ya ci 42 da bayar da tara aka zura a raga a wasa 39 a Premier League.
- ‘Dalilin da Tinubu ya yi wa dukkanin Jakadun Najeriya kiranye’
- Ba za mu janye dokar hana dalibai mata sanya abaya a makarantu ba — Faransa
Ke nan ya zama na farko da yake da hannu a zura kwallo 50 ko fiye da haka a babbar gasar tamaula ta Ingila, bayan Andrew Cole da ya yi wannan bajintar amma a karawa 43.
Haaland ya cimma wannan kadami ne yayin da Manchester City ta caskara Fulham 5-1 a wasan mako na huɗu a gasar Premier League ranar Asabar a filin wasanta na Etihad.
City ce ta fara cin kwallo ta hannun Julian Alvarez a minti na 31 da fara tamaula, amma minti biyu tsakani Tim Ream ya farke wa Fulham.
Daf da za su je hutu ne City ta kara na biyu ta hannun Nathan Ake a fafatawar.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Erling Haaland ya ƙara na uku, sannan ya ci na huɗu a bugun fenariti.
Haaland – wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan UEFA na bana a makon da ya gabata – ya kuma ci na biyar daf da za a tashi, kwallo uku rigis da ya ci a ranar Lahadi, sannan na shida da fara kakar bana.
Wasan dai shi ne karo na 15 da City ta doke Fulham a tarihin, irin yawan nasarar da ƙungiyar Etihad ta yi kenan a kan Watforrd.
Wasa na 21 da Fulham ta yi a Etihad ba ta samu nasara ba tun bayan 3-1 da ci a Afirilun 2009.
City za ta ziyarci West Ham a wasan mako na biyar ranar 16 ga watan Satumba, yayin da Fulham za ta karbi bakuncin Luton.
Wasa na biyu a jere kenan da Pep Guradiola bai ja ragamar City ba a Premier, wanda ke jinya, amma zai halarci wasan gaba, lokacin ya gama jinya.