Haaland ya zama dan kwallon da babu kamarsa a Firimiyar Ingila a bana
A bangaren mata, ’yar kwallon Chelsea, Sam Kerr ce ta samu kyautar a karo na biyu a jere.
An sanar da dan wasan Manchester City, Erling Haaland a matsayin gwarzon dan kwallon kafa na bana wanda kungiyar marubuta kwallon kafa ta Ingila ke bayarwa.
Haaland ya haskaka sosai a kakar wasa ta bana inda kawo yanzu ya zura kwallo 52 a duka gasar da ya buga.
- Angola ta zarce Najeriya a hako danyen man fetur —OPEC
- Dalilai 8 da ke tunkuda mutane zuwa ɗabi’ar Luwaɗi da Maɗigo
Rawar da ya taka ta taimaka wa tawagar Pep Guardiola kai wa mataki na farko a teburin gasar Firimiyar Ingila da kuma kai wa matakin kusa da karshe a gasar Zakarun Turai.
Haaland mai shekaru 22 ya samu kashi 82 cikin 100 na kuri’ar da aka kada domin bayar da kyautar.
’Yan wasan Arsenal — Bukayo Saka da kuma Martin Odegaard — su ne suka yi na biyu da na uku, sai kuma Kevin De Bruyne na Manchester City ya zo na hudu a yayin da dan kwallon Manchester United Marcus Rashford ya kasance na biyar.
A bangaren mata, ’yar kwallon Chelsea, Sam Kerr ce ta samu kyautar a karo na biyu a jere.