Haba Babangida Kakaki kamar ba a Kaduna kake zaune ba

Mai karatu yau zai yi mamaki a kan inda makalar tawa ta mayar da hankali, ba don komai ba kuwa, sai don a tsawon tarihin wannan rubutu da nake yi, ban iya tuna wata rana da na mayar da martini a kan abokin aiki na jarida ba, sai a yau. Ina nufin na sha mayar […]

Haba Babangida Kakaki kamar ba a Kaduna kake zaune ba
Haba Babangida Kakaki kamar ba a Kaduna kake zaune ba

Mai karatu yau zai yi mamaki a kan inda makalar tawa ta mayar da hankali, ba don komai ba kuwa, sai don a tsawon tarihin wannan rubutu da nake yi, ban iya tuna wata rana da na mayar da martini a kan abokin aiki na jarida ba, sai a yau. Ina nufin na sha mayar da martani a kan rubuce-rubuce ko kalaman `yan siyasa walau masu rike da madafun iko ko marasa mukaman madafun iko, amma dai ban taba yi ba a kan wani rubutu na ra`ayin wani abokin aiki. 

A wannan karon na ga ya zama wajibi in yi, saboda yadda na ga wani kanena koma in ce dana kuma abokin aiki, Editan jaridar The Bottomline, wato Malam Babangida Kakaki ya yi rubutu a Jaridar Leadership hausa ta ranar Juma`ar da ta gabata mai kanun “GIDAN RADIYON FRCN: LADAN SALIHU A SIKELI”, inda ya bi sahun dimbin nasarorin tafiyar da mulkin (kamar yadda ya kira su) da Malam Ladan Salihu ya samu cikin mulkinsa na shekara dada da watanni hudu, a matsayin Darakta Janar na Gidan Radiyon FRCN, Abuja. Rubuce-rubuce irin wadannan suna daga cikin `yancin da tsarin mulki ya ba kowane dan kasa na fadin albarkacin baki, musamman rubutu irin na dan jarida da ake tsammanin ya fada wa mutane gaskiya, a duk abin da zai rubuta ko ya fada masu ba ya rika shaidar zur ba.
Gaba dayan makala da ta kunshi cikakken shafi, Malam Kakakiya mayar da hankali ne waje kola Malam Salihu a zamansa na Darakta Janar na FRCN, har ma cewa ya yi “A halin yanzu in ban da daidaikun shugababannin da suka shude, wadanda za a iya kidaya su, babu wani shugaban Hukumar da ya aikata ayyukan alherin da Malam Ladan ya aiwatar a cikin dan karamin lokaci.” A nan Malam Kakaki bai iya kawo sunayen shugabannin da suka gabata ban a baya-baya da yake nufi da Malam Ladan Salihu ya fi su ba, sai dai ya yi fyadin `yan kadanya. Ai kamata ya yi ya fito karara ya fadi cewa Malam Ladan Salihu ya fi Mista Calbin Ejiofor ko Mista Edie Iroh, ko Barista Yusuf Nuhu.
Ya kamata Malam Kakaki ya sa ni cewa a zamanin Mista Edie Iroh, a zangon farko na shugaba Obasanjo, shi ya kirkiro a kafa tashoshin Radiyo na FM, na gwamnatin tarayya, kuma tun yana kan shugabanci ya fara ganin an bude wasu daga cikinsu kamar ta Kano. Barista Yusuf Nuhu, kuwa a cikin wa`adinsa na shekaru hudu 2009 zuwa 2013, ya ci gaba da bude wasu kamar na jihar Kebbi da Jigawa. A kan maganar dauka da karin girma ga ma`aikatan Gidajen Radiyon FRCN, ko shakka babu Malam Ladan ya taka ta shi irin rawar, gwargwadon zarafi, wadda dama haka aiki ya gada. Amma ko Malam Kakai ya san cewa a kan ma`aikata Malam Ladan ya bar wani mummunan tarihin da ba a taba yi ba a cikin tarihin kafuwar tashar ta Kaduna yau shekaru 53, inda ya sa hannu aka yi korar kare, ta ba fansho bare garatute ga wasu ma`aikata uku da kowannensu ba wanda bai haura shekaru 26, ba, yana aiki da tashar ta Kaduna, wani ma daga cikinsu shekaru biyu suka rage masa ya yi ritaya, ta ya samu 35, yana aiki da tashar ta Kaduna.
Abin da ya sa na kira korar da korar kare, bai wuce irin sanin da na yi ba na cewa koda gwamnatocin Janar Murtala da Obasanjo (1975 zuwa 1979) da suka fara bullo da tsarin korar ma`aikata da sunan gyara aikin gwamnati, ba inda suka kori ma`aikacin da ya kai irin wadancan tsawon shekara na irin wadanda Malam Ladan ya kora ba tare da an ba su kudaden fensho da gagatute ba. Sanina da aikin gwamnati, babban laifin da zai sanya a yi wa ma`aikacin gwamnatin da ya samu irin wadancan shekaru korar kare, shi ne kamar na sata ko fashi da makami ko laifin kisan kai ko wani babban laifi makamancin wadannan da na riga na ambata. Dukkan mutanen uku da Malam Ladan din ya kora, ba daya daga cikinsu da aka samu da aikata makamantan wadannan laifuffuka, ko kusa ba cewa ni ke ba su yi laifi ba, amma laifuffukan da ake zarginsu da aikatawa, laifuffuka ne da suka zama ruwan dare a cikin tashoshin gidaje Radiyon tarayya da sauran ma`aikatu da Hukumomin gwamnatoci, da tanade-tanaden aiki zai iya kula da su, ba sai ta kai ga korar kare ba.
Ma`aikatan uku sune Abubakar Abdurraham tsohon Janar Manaja na tashar FM da ke Gusau mai shekaru 33, yana aiki da Haruna Aliyu Hadeja shi ma tsohon Janar Manaja na tashar FM da ke Kano mai shekaru kusan 26 da Malam Falalu Mohammed shi ma mai shekaru 26 da aiki.
Malam Kakaki kuma ya fadi cewa saboda ba a son Malam Ladan ya hau kujerar Darakta Janar, ya sanya aka ki mika masa ragamar mulki aka ba na kasa da shi wannan ba gaskiya ba ne.Shi Malam Ladan ya san akwai Daraktoci uku da ke gabansa cikinsu kuwa har da Madam Bola Agbola. Wani batun da Malam Kakaki ya yi na nasarorin da Malam Ladan ya yi shi ne irin yadda bai bi sahun Kafofin yada labarai irin na gidan Talabijin na kasa wato NTA da AIT, wajen yada farfagandar karya da cin mutunci a cikin yakin neman zabe ga jam`iyyar adawa ta APC a lokacin da dan takararta na neman shugabancin kasa ,shugaban kasa a yau wato Alhaji Muhammadu Buhari. Ma`ana dai yana nufin ya ce Malam Ladan ya yi adalci. Mai yiwuwa Malam Kakaki ba ya da labarin yadda dan takarar neman mukamin Gwamnan jihar Kaduna na jam`iyyar APC, Gwamnan jihar a yau Malam Nasiru eL-Rufa`i da jam`iyyarsa suka kwashe da tashar ta Kaduna ba a lokacin yakin neman zabe ba bayan ya zama Gwamna.
Akwai kuma batun irin yadda shugaban jam`iyyar APC na jiharmu ta Katsina (har da shi Malam Kakaki), Dokta Mustapha Inuwa wanda bayan tashar Kaduna ta ki karbar kudin tallar su ta yakin neman zabe, har koke ya kai Majalisar Dokoki ta kasa da Hukumar kula da tashoshin yada labarai ta kasa, wato NBC, koken da ya sanya sai da Malam Ladan ya gurfana gaban `yan Majalisar Dokokin na kasa. Malam Kakaki ba ya da labarin gagarumin taron da aka yi da wani babban jami`in tsohon Shugaban kasa da Janar Manajojin tashoshin FM na jihohin Arewa da masu gbatar da shirye-shiryen siyasa da Daraktoci shiyya da ke Arewa da shi kanshi Malam Ladan a Abuja inda aka tsara yadda lalle kada a ba da kafa komai kankantarta ga jam`iyyar adawa ta APC a cikin harkokin yakin neman zaben, inda ya zama dole a saurare su, to a ba su lokacin da ba shi da wani muhimmanci ga masu sauraro.
Mai karatu akwai batutuwa da dama da nake son in kawo a kan wannan tsokaci na abokin aiki Malam Kakaki, amma fili ba zai ba da dama ba. Amma babban abin lura a nan, ya ci a ce kafin Malam Kakaki ya yi wancan rubutu, a ce ya yi kyakkyawan bincike tsakankanin abokan aikinsa na gidan Radiyon Kaduna inda na san nan yake da zama, domin kusanci na daya daga cikin ka`idojin da aka a jiye a cikin aikin jarida na iya samun hakikanin labari kuma da dumi-duminsa, sabanin wanda ke nesa. Amma daga dukkan alamu Malam Kakaki, bai yi amfani da wannan koyarwa ba. A da dai ina kallon Malam Kakaki kamar wani dan gwagwarmaya kamar yadda aikin na jarida ya gada, amma da wannan rubutu ina ga kamar yana neman ya saki layi, idan kuwa haka ne, to ina ba shi shawara, shi da ire-irensa matasa da ake fatan su gaji wannan gwagwarmaya, da su yi kokarin kauce wa irin haka. Masu iya magana suna cewa “mutunci madara ne idan ya zube ba`a kwashe shi”.