Haba Buba Galadima!
Salam edita. Da fatan kana lafiya, Allah Yasa haka amin. A yau na shigo filin ne domin ka ba ni dama in yi dan gajeren tsokaci a kan tsohon na hannun daman Shugaba Buhari wato Injiniya Buba Galadima. Haba Buba Galadima! Ai kamata ya yi ka fito fili ka bayyana canja shekarka zuwa jam’iyyar adawa […]
Salam edita. Da fatan kana lafiya, Allah Yasa haka amin. A yau na shigo filin ne domin ka ba ni dama in yi dan gajeren tsokaci a kan tsohon na hannun daman Shugaba Buhari wato Injiniya Buba Galadima. Haba Buba Galadima! Ai kamata ya yi ka fito fili ka bayyana canja shekarka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP a maimakon cigaba da fakewa da guzuma kana harbin karsana. Domin kuwa ko karamin yaro da bai mallaki hankalinsa ba ya ji kalamanka, to ya san PDP kake yi wa aiki da sunan kai dan APC ne! Shin me zai hana ka fito fili ka yi adawarka tunda dai tsarin mulkin Najeriya bai haramta maka yin hakan ba? A ƙarshe ina so ka sani cewa sukar gwamnatin Buhari da kake ido bude ba zai sa ka cimma burinka na siyasa ba. Domin a matsayinka na dattijo a Arewacin Najeriya hakan zai kara jawo maka karan tsana ga mu ‘yan Arewa da muka san muhimmancin mulkin Shugaba Buhari a Najeriya.
Daga Ashiru Lawal Nagoma RuwanƁore Gusau (Ɗan Kishin Talaka). 08128828467.