Haba, Fasto Bakare! 01

Kiran da Fasto Tunde Bakare, wanda ya rufa wa Janar Buhari baya a zaben 2011, don dage zabukka masu zuwa har na tsawon shekaru biyu, saboda abin da ya kira hali da yanayin da kasar ke ciki, al’amari ne mai daure kai matuka. Abin da kuma ya kara ba ‘yan Najeriya mamaki, shi ne, yadda […]

Haba, Fasto Bakare! 01
Haba, Fasto Bakare! 01

Kiran da Fasto Tunde Bakare, wanda ya rufa wa Janar Buhari baya a zaben 2011, don dage zabukka masu zuwa har na tsawon shekaru biyu, saboda abin da ya kira hali da yanayin da kasar ke ciki, al’amari ne mai daure kai matuka. Abin da kuma ya kara ba ‘yan Najeriya mamaki, shi ne, yadda ya kawo shawarar cewa a kafa gwamnatin wucin-gadi, wacce za ta bai wa Shugaba Goodluck Jonathan sukunin ci gaba da mulki, har na tsawon wasu shekaru biyu masu zuwa. A cewar wannan Fasto yin haka zai bayar da damar yin gyararraki ga tsarin siyasar kasar nan, wanda duk da cewa na federaliyya ne, amma bai dace ba da yadda ake gudanar harkokin mulkin kasar ba. Sa’annan kuma ya ce wajibi ne kafin a yi zabubbuka a daidaita yanayin tattalin arzikin kasar nan, yadda kowane bangare zai samar da abin da zai habaka arzikin kasa, maimakon dogaro da kasar ta yi kacokan kan wani abin da wani bangare guda ne kadai ke samarwa. Haka nan kuma Faston ya so a ce an dage zabubbukan ne har sai an warware matsalar tankiyar da ake ta yi game da yawan al’ummar kasar nan, sa’annan kuma a ba hukumar zabe damar cin gashin kanta yadda ya kamata. 

To amma ai wadannan zantuttukan soki-burutsu ne, domin kuwa wasu dabaru ne kawai na kara wa Shugaba Jonathan wa’adin wasu shekaru biyu a kaikaice, domin kamar yadda wasu masu irin wannan ra’ayin ke gani hakan shi ne zai ba shi damar yin cikakken nazarin rahoton taron kasa da aka yi a bara da niyyar aiwatar da munanan shawarwarin da zai yi illa ga wasu sassan kasar nan da kuma abubuwan da jama’a suka yi imani da su.
To, amma wadannan shawarwari na Fasto Bakare ba su da tushe, balle makama a tsarin mulkin kasar nan, kuma suna iya janyo bala’in da zai tayar da zaune tsaye a kasar har ma gudanar da harkokin mulki su gagara, su kuma tsaya cik, a rasa wanne ne, ba wanne-ne ba. Saboda haka nan hankali ba zai amince da su ba, kuma makomarsu shi ne kwandon shara kawai, domin can ne suka fi dacewa. Wadannan shawarwarin dai saba wa sassa da yawa na kundin tsarin mulkin 1979 (wanda aka yi wa kwaskwarima), musamman ma sashi na 135 sakin layuka na daya da biyu da kuma uku, wadanda suka fayyace ka’idojin sauka daga mulki ga zababben shugaba, da suka hada da rashin nasara a wajen zabe, har hakan ya sanya aka rantsar da wani a makwafinsa, ko kuma idan ya mutu a bakin aiki ko idan wa’adinsa na barin aikin don kashin kansa ya cika. Haka nan kuma wannan sashe na kundin tsarin mulki ya nuna wajibcin saukar zababben shugaba daga mulki bayan cikan wa’adinsa na shekaru hudu daga ranar da aka rantsar da shi a karo na farko.
Baicin haka kuma sashe na 135 sakin layi na uku ya fayyace cewa idan har ana yaki da kasar, kuma hakan ya shafi wani bangarenta, kuma Shugaban kasar ya fahimci cewa hakan na iya hana gudanar da zabe, to Majalisar kasa na iya yin kudurin da zai tsawaita wa’adin gwamnati akai-akai, amma hakan ba zai wuce watanni shida ba a tashi guda.
To idan aka yi la’akari da haka sai a fahimci cewa shawara ko kiran da Fasto Bakare ya yi don kafa gwamnatin wucin-gadi ba su da wani hurumi a cikin kundin tsarin mulkin kasar nan.
Abin da kawai zai sa shawararsa ta yi tasiri shi ne idan wata kasa na yaki da Najeriya, to amma ba haka al’amarin ya kasance ba a halin yanzu. Abin da ke faruwa yanzu haka a kasar nan ta’addanci wasu tsageru ne, saboda haka babu wani dalili ko hujjar da za ta kai ga dage zabubbukan da ake fuskanta a halin yanzu. Saboda haka nan amincewa da wannan shawarar tamkar yi wa kundin tsarin mulki karan tsaye ne, kuma babu wanda zai goyi bayan haka, domin kuwa ba mai yiwuwa ba ne. Wannan dai al’amari ne da kowane ne ya zama shugaban kasa bayan zaben watan Fabrairu da zai iya magancewa cikin ruwan sanyi. Batun cusa shawarwarin da suka taso sakamakon taron kasa a cikin harkokin yin gyararraki ga kundin tsarin mulki, abu ne da ya shafi majalisun kasa, kuma za su tunkare shi a daidai lokacin da ya dace.
Wannan ne dai karo na hudu da ake samun sukunin canjin gwamnatocin dimokuradiyya , saboda haka nan wajibi ne mu yi kaffa-kaffa a wanan lokacin, mu guji yin aiki da gurguwar shawarar da za ta kai ‘kilu ta ja Bau,’ ‘garin neman kiba a nemo rama.’
Gwamnatin wucin gadi, walau a zamanin mulkin soja ko kuma na farar hula ba ta taba yin tasiri ba a kasar nan, mun ga yadda ta Cif Ernest Shonekan ta wanye, saboda haka nan tun da an yi wankan wuta sau guda ba kuma za a sake yafawa ba. An sha kai ruwa rana kafin a ga bayan mulkin soja a kasar nan, kuma tunda ga shi nan bisa ga dukkan alamu dimokuradiyyar ta kai shekaru 16, ta kuma kama hanyar dorewa, to bai kamata ba mu tadiye ta mu da kammu.
’Yan Najeriya dai a yanzu a shirye suke su yi amfani da wannan damar da dimokuradiyyar da ake tunkaho da ita ta samar don wancakalar da gwamnatin da ba su ga alfanunta ba a gare sub a. To don me wani can zai dage wajen kawo shawarwarin da za su mayar da hannun agogo baya? Ta yin haka ne kawai za mu iya magance dukkan wadancan matsalolin da Fasto Bakare ya zayyana a matsayin hujjarsa ta gabatar da waccan gurguwar shawarar. Ai an ce sai da ciwo ne za a iya kawar da ciwo, to a shirye kowa da kowa yake don ganin bayan wannan gwamnatin da ta kasa tsinana wa jama’a komai, wacce kuma ta jefa cikin matsalolin da suka haddasa zubar da jini da hawaye a ko da yaushe. Allah ya kiyaye.