Haba kungiyar ASUU, a rika sara ana duban bakin gatari

“Wasu malaman kan koyar a jami’o’i uku zuwa hudu, sabanin yadda aka amince masu.”

Haba kungiyar ASUU, a rika sara ana duban bakin gatari

Wakilan Gwamnatin Tarayya da na ASUU yayin wata tattaunawa

Idan har zuwa wannan lokaci da mai karatu yake karanta wannan makala, ba a samu cim ma wata yarjejeniya ba tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa ASUU a kan yajin aikin gargadi da jan kunne na wata guda da kungiyar ta fara tun a ranar 14 ga watan Fabrairun da ya gabata, yau ke nan an shiga kwanaki 19, ’yan kungiyar suna yajin aikin.

Yajin aikin ’yan kungiyar ta ASUU a kasar nan yana da dadadden tarihi da masu bibiyar sa suka kiyasta yakai kusan shekara 40, ana fama da shi daga lokaci zuwa lokaci, amma dawowar mulkin demokradiyya a shekarar 1999, shi ya fi ta’azzara, inda ’yan kungiyar suka tafi yajin aiki sau 16, inda suka dauki kwana 1,297, kwatankwacin shekara uku da wata shidda ke nan sukai suna yajin aikin.

Akwai kuma yajin aikin da ’yan kungiyar ta ASUU suka yi tsakanin watan Maris din shekarar 2020 zuwa Disambar shekarar bara a lokacin da ake zaman kulle na Kwarona. Nan ma sun samu wasu watanni goma.

A wannan Jamhuriyyar, dala-dalar yajin aikin ’yan kungiyar ta ASUU, ya kasance kamar haka. A shekarar 1999, sun shafe kwana 150, a shekarar 2001 sun samu kwana 90, yayin da a shekarar 2002, kwana 14, kwana 180, ’yan kungiyar ta ASUU suka shafe a shekarar 2003.

Masu bibiyar yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’o’in sun tabbatar da cewa, a shekarar 2004 Kungiyar ba ta shiga yajin aiki ba, amma a shekarar 2005 ta dana na kwana 3.

A shekarar 2006, sun yi yajin aikin kwana 7, yayin da a shekarar 2007 sukai yajin aikin kwana 90 a 2008, kwana 7 suka dana a zaman yajin aiki. A shekarar 2009 da 2010, sun yi yajin aikin kwanaki 120 da 157, bi-da-bi.

A shekarar 2011 kwana 190 suka shafe suna yajin aiki. Kodayake a shekarar 2012, ’yan kungiyar ta ASUU ba su yi yajin aiki ko da na minti daya ba, amma a shekarar 2013, sun shafe kwana 150 suna yajin aiki.

Kwana 7 ASUU ta yi tana yajin aiki a shekarar 2016, bayan sararawar kusan shekara uku, sai a shekarar 2017 da ta samu kwana 35, yayin da a shekarar 2018 zuwa 2019 kwana 97 suka shafe suna yajin aiki.

Kasancewar shekarar 2020, shekara ce da annobar Kwarona ta addabi kasashen duniya, ciki kuwa har da kasar nan, amma masu bin sawun yajin aikin ASUU sun tabbatar da cewa, tsakanin 23 ga watan Maris zuwa 23 ga Disambar shekarar bara, duk da zaman kulle da ake ciki, ‘yan kungiyar ta ASUU suna cikin yajin aiki.

A bana kuma ga wanda ake ciki na wata guda a zaman gargadi ko jan kunne, bayan shi kuma Allah Ne kadai Ya san abin da ka iya biyo baya na wani yajin aikin da ’yan kungiyar ta ASUU ka iya tsunduma, muddin ba su samu biyan bukatar da suke muradi ba.

Kusan a kan muhimman bukatu uku kungiyar ta ASUU ta makale a kan yawan yajin aikin nata, ko da akwai wasu. Na farko batun ba Jami’o’in ’yancin cin gashin kai, ma’ana a bar mahukuntan kowace jami’a su rika tafiyar da jami’o’insu a bisa ga nasu tsarin kamar yadda ASUU ta ce ana tafiyar da jami’o’in gwamnatoci a kasashen waje.

Na biyu, lalle Gwamnatin Tarayya ta rika samar da isassun kudade kuma a kan kari don tafiyarwar yau da kullum da na ayyukan raya kasa da na bincike-bincike da na sauran bukatu ga jami’o’in.

Bukatar ASUU ta uku, ita ce neman a biya ‘ya’yanta dimbin kudaden alawus-alawus na wasu ayyuka na musamman da sukan gudanar a cikin ayyukansu na koyarwa da bincike. A ’yar tawa gurguwar fahimtar a yau ba sai gobe ba, bana jin akwai wasu hukumomi da suke mallakar Gwamnatin Tarayya dari bisa dari da suke da ‘yancin cin gashin kai kamar jami’o’in kasar nan.

Alal misali, yanzu jami’o’in da suke zaba wa kansu shugabanni, sabanin da a baya ake zabar mutum uku a tura wa Shugaban Kasa ya zabi daya. Na biyu, Malaman jami’o’in suna da cikakken ‘yancin su koyar kuma a biya su a wasu jami’o’i biyu, bayan jami’ar da suke koyarwa ana kuma biyan su rabin tsuran albashin da suke dauka a jami’o’insu.

Zuwa yanzu rahotanni sun tabbatar da cewa, wasu malaman kan koyar a jami’o’i uku zuwa hudu, sabanin yadda Gwamnatin Tarayyar ta amince masu. Mai karatu ka ga ke nan za su iya samun akalla karin kwatankwacin rabi ko biyu bisa uku ko ma fi na ainahin albashinsu na duk wata.

Bayan haka, wasu Malaman jami’o’i kan shiga ayyukan ba da shawarwari ko tuntuba ko na gabatar da wasu makaloli ga gwamnatoci ko hukumominsu ko na kamfanoni masu zaman kansu, koma na mutum da mutum, ba tare da ma la’akari da makomar aikinsu na koyar da dalibai ba.

Kai wasu binciken ma dalibansu sukan sa su yi masu da sunan fannin darasinsu alhali kuma na neman dari da kwabon malaman ne. Rashin fili ba zai ba ni damar in kawo jerin irin dimbin ayyukan kashin kai da Malaman jami’o’in kasar nan suke, baya ga tsunduma cikin harkokin siyasa da suke yi duk da sunan ‘yanci.

Ko kusa ba cewa nake ba Gwamnatin Tarayya na kula da fannin ilimin jami’o’in kasar nan kamar yadda ya kamata ba, amma kuma nacin yajin aiki irin na Malaman jami’o’in kasar nan ya yi kazancewar da sai dai neman dauki daga Allah.

Wasu ’yan kasa na ganin ya kamata yadda kungiyar ta ASUU ta zama babbar kungiyar mai karfin fada a ji a kasar nan, ta mayar da hankalinta wajen ganin tana tilasta wa gwamnatoci da sauran hukumomi baki daya a kan yadda za a gyara fannin ilimi tun daga tushe wato tun daga kan ilimin Firamare zuwa na Sakandare, fannin da gaba daya a tabarbare yake tun a shekaran jiya waccan.

Ina cikin rubuta wannan makala sai ga labarin sauran ‘yan kungiyoyi uku da ke aiki a jami’o’in kasar nan wato Kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’i ta kasa wato SSANU da Kungiyar Ma’aikatan da ba Malamai ba da ta Manyan Makarantun Kasar nan wato NASU da kuma ta ‘yan Kungiyar Malaman Fasaha na Manyan Makarantu ta Kasa wato NAAT, duk sun yi barazanar su ma za su shiga yajin aiki, muddin gwamnatin ba ta biya masu bukatunsu ba.

Ita ma Kungiyar Daliban Najeriya ta cikasa alkawarinta na gudanar da zangazangar lumana a ranar Litinin da ta gabata a dukkan manyan biranen kasar nan, a zaman matsin lamba ga Gwamnatin Tarayya.

A yayin zangazangar daliban sun ragargaji Gwamnatin Tarayya da Kungiyar ta ASUU a kan wannan kiki-kaka. Tabbas, kusan ‘yan kasa baki daya, musamman iyayen dalibai da daliban kansu sun gaji da wannan danbarwa da ta ki ci, ta ki cinyewa.

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele