Haba Sanata Kwankwaso ina aka taba haka aka zauna lafiya?
Ni, a nawa dan karamin tunanin zuwa yanzu lokaci ya yi da shugabannin da suke tafiyar da mulkin wannan jamhuriyar da take neman shekaru ashirin (20) da farawa, su fara sanin cewa don ka yi nune an zabi mutum, ba hujja ba ce kuma ka dawo ka ce lallai sai abin da kake so za […]
Ni, a nawa dan karamin tunanin zuwa yanzu lokaci ya yi da shugabannin da suke tafiyar da mulkin wannan jamhuriyar da take neman shekaru ashirin (20) da farawa, su fara sanin cewa don ka yi nune an zabi mutum, ba hujja ba ce kuma ka dawo ka ce lallai sai abin da kake so za a yi cikin gudanar da mulkin. Ba don komai ba sai don ganin rikicin da aka yi a jamhuriya ta biyu Oktoba 1979 zuwa Disamba 1983, tsakanin marigayi Malam Aminu Kano madugun jam`iyyar PRP na kasa baki daya da gwamnonin jam`iyyar na tsofaffin jihohin Kano da Kaduna, wato marigayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi da Alhaji Balarabe Musa.
A wancan lokaci, babban abin da ya haddasa rigimar da har marigayi Malam Aminu Kano ya koma kushewarsa a shekarar 1983, ba a ga maciji tsakaninsa da gwamnonin bai wuce irin yadda shugabancin jam`iyyar PRP din ya ja daga ya ce ga irin mutanen da za a nada a matsayin Kwamishinoni da sauran masu rike da madafun iko a cikin gwamnatocin, umurnin da gwamnonin biyu suka sa kafa suka shure, kuma suka ci gaba da yin gaban kansu cikin gudanar da mulki, karshe ma dai suka shiga taron kungiyoyin gwamnoni 12, `yan gabadai-gabadai na jam`iyyun UPN da GNPP da NPP, daga wancan rigima ce aka samo tarihin santsi da tabo, tabo bangaren magoya bayan Malam Aminu Kano, santsi bangaren Gwamna Rimi a cikin rushashshiyar jam`iyyar PRP. Har gobe wadancan bangarori biyu suna da matukar tasiri a cikin siyasar Jihar Kano.
Da aka fara wannan jamhuriyar a shekarar 1999, daga Jihar Barno aka fara ganin siyasar bijire wa ubangidan da ya yi nadi a kan wanda aka nada, lokacin da Sanata Ali Modu Shariff, shi kadai, yana zaman dan Majalisar Dattawa ya yunkuro a shekarar 2003, ya kwace jam`iyyarsu ta APP, daga hannun gwamnan jihar na lokacin marigayi Malah Kachallah, wanda ala tilas ya canja sheka zuwa jam`iyyar AD, inda ya yi takarar neman sake zama gwamnan a karo na biyu, amma ubangidan nasa Sanata Sheriff ya kada shi a neman mukamin gwamnan jihar ta Borno a zaben shekarar 2003.
Haka wannan rigima ta kaure ta kuma yi kamari a shekarar 2003, tsakanin Gwamnan Jihar Kwara a inuwar jam`iyyar APP, marigayi Alhaji Muhammadu Lawal da jagoran siyarar tsohuwar Jihar Kwara, Sanata Abubakar Bukola Saraki, inda a lokacin da Dattijo Saraki ya ma fice daga jam`iyyar APP, ya koma PDP, ya kuma tsayar da dansa shugaban Majalisar Dattawa mai ci yanzu Sanata Bukola Saraki, wanda ya yi nasara a kan Gwamna Muhammadu Lawal. Sai ga shi tsakanin da da uban ba a karke lafiya ba, ta yadda har sai da mutanen gari suka rinka shiga tsakaninsu. Kai karewa ma da karau a zaben shekarar 2011, bayan Sanata Bukola ya kammala wa`adinsa na zango na biyu a shekarar 2011, da mahaifinsu, ya nemi Gwamna Saraki, ya ba kanwarsa Sanata Bisola Saraki takarar gwamnan jihar, amma ya ki, sai mahaifin ya sake dauko wata jam`iyyar ya tsayar da kanwar a zaman mai neman gwamnan jihar ta Kwara, amma dan takarar da Gwamna Saraki ya tsayar, Alhaji Abdulfatah Ahmed, karshe shi ya lashe zaben na shekarar 2011.
Kar ka yi batun yadda aka karke tsakanin tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Sanata Ahmed Sani da mataimakinsa Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi, wanda shi ne tsohon mataimakin gwamna na farko a tarihin mulkin siyasar kasar nan da gwamnansa ya fara mika wa takarar neman ya gaje shi a shekarar 2007, bayan sun kammala wa`adin zangonsu na biyu lami lafiya. Amma shi din ma aka rabu baran-baran kowa ya kama gabansa, daga karshe har zuwa yau dinnan tutar siyasar Sanata Ahmed Sani ke kadawa a duk fadin jihar ta Zamfara.
Mai karatu na kawo maka `yan wadannan bayanai ne a zaman matashiya a kan irin yadda siyasar nune tsakanin Ubangida da yaron gidan da aka yii nune a kansa ya kuma yi nasarar zama Maigida a kan yadda take kasancewa. Bari in koma a kan jigon abin da nike son yin tsokaci a yau. Koda dai akwai wata alaka ta kut-da-kut tsakanin Sanata Dokta Rabi`u Kwankwaso da Gwamna Ganduje, kafin haduwarsu ta tafiya tare a zaman gwamna da mataimakinsa a bullar wannan jamhuriya, wato 1998, to kuwa ba ta kai ta a je a karas ba, kuma ba kowa ya san ta ba. Ga dai akasarin mutanen Jihar Kano abin da suka sa ni bai wuce manyan siyasar jihar biyu a shekarar 1999, sun nemi su tsaya wa jam`iyyar PDP takarar neman mukamin Gwamnan Jihar Kano, inda Dokta Kwankwaso ya zo na daya, ya yin da Dokta Ganduje ya zo na biyu. Don kwadayin samun nasara, sai iyayen jam`iyyar suka yanke shawarar hadasu a zaman dan takara da mataimakinsa cikin neman mukamin gwamna. Allah kuma ya ba su nasarar zaben. Koda suka fadi a zaben 2003, sun ci gaba da tafiyar siyasa tare, har Allah Ya sake dawo da su gwamnati a shekarar 2011.
Duk zaman da suka yi a wadancan shekaru 16, da dadi ba dadi Gwamna Ganduje yana biye da Sanata Kwankwaso sau da kafa, duk kuwa da irin yadda ‘yan gaza gani masu neman gindin zama a wajen Gwamna Kwankwaso ba irin yadda ba su yi ba wajen ganin sun shiga tsakaninsu, amma Allah bai sa sun yi nasarar raba su ba, bisa ga irin hakuri da juriya da neman cimma buri, bai sa Gwamna Ganduje ya bar tafiyar Sanata Kwankwaso. Haka ya yi ta binsa tamfar rakumi da akala, har Allah Ya sa suka koma sabuwar jam’iyyar APC a shekarar 2014, inda Gwamna Kwankwaso ya ga ba sarki sai Allah ya ba Gwamna Ganduje takarar zama gwamna a zaben shekarar 2015.
A lokacin da Sanata Kwankwaso yake kan mulki ba irin abin da bai ba a zaman giyar mulki, har ta kai anai masa kirarin “Mai takalmin karfe, kowa ka taka ya taku.” Kodayake da rana daya Sanata Kwankwaso bai taba boye aniyarsa ba, ta ya dawo Kano ya yaki magajinsa, muddin magajin ya kauce daga kan akidar darikar siyasar su ta Kwankwasiyya, kamar yadda ya fadi a hirar da aka yi da shi a cikin watan Afrilun 2015, a cikin shirin Barka da Hantsi na gidan Radiyo Freedom da ke Kano.
Tashin-tashinayar da ta taso a kwanannan nan an hana Sanata Kwankwaso shigowa Kano don ya kaddamar da yakin neman zaben shugabanni da kansiloli na kananan hukumomin jiha da za a yi gobe in Allah Ya kaimu, bisa ga shawarar da rundunar ‘yan sandan jihar suka ba shi, wadda ta kai ya janye, da yanzu kuma yadda Majalisar Dattijai ta umarci Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar nan da lallai ya ba Sanata Kwankwaso dukkan kariyar tsaro yadda ya kamata don ya shigo Kano ya sadu da magoya bayansa. Duk wasu abubuwa ne da ya kamata Gwamna Kwankwaso da shugabanni irinsa zuwa yanzu su farka daga barcin da suke su kuma yi korkarin fita daga giyar mulki, su gane cewa Zamani kowa da nasa don haka su rinka girma tare da sakar wa wadanda suka gajesu mara, su yi mulki yadda suke so, kamar yadda su suka yi. Haka shi ne zaman lafiyarsu da mutuncinsu da nasararsu a kan abin da suke son su cimmawa na siyasa muddin dai don ci gaban mutane suke siyasa.