Habasha da Eritiriya sun bude iyakarsu bayan shekara 20
A ranar Talata da ta gabata ce aka bude babbar iyakar Habasha da Eritiriya bayan shekara 20 da rufe ta, sakamakon yaki da rikici a tsakaninsu. Shugabannin kasashen biyu suna daga cikin manyan bakin da suka halarci bude babbar kan iyakar a Burre, wanda hakan na daya daga cikin alamun samun maslaha a tsakaninsu. Kuma […]

A ranar Talata da ta gabata ce aka bude babbar iyakar Habasha da Eritiriya bayan shekara 20 da rufe ta, sakamakon yaki da rikici a tsakaninsu.
Shugabannin kasashen biyu suna daga cikin manyan bakin da suka halarci bude babbar kan iyakar a Burre, wanda hakan na daya daga cikin alamun samun maslaha a tsakaninsu.
Kuma wannan lamari zai saukaka wa mutanen Habasha zuwa tashar jiragen ruwa ta Assab kamar BBC ya ruwaito.
Kuma za a sake bude wata iyakar da ta hada kasashen biyu da ke kusa da garin Zalambessa a Habasha.
Bude iyakar ta faru ne bayan a watan Yuli, Firayi Ministan Habasha Abiy Ahmed da Shugaban Eritiriya Isaias Afwerki sun sa hannu a wata yarjejeniyar dawo da zaman lafiya da harkokin kasuwanci a tsakaninsu.
Bikin bude babbar iyakar, wanda ya zama makasudin hada kasashen biyu, ya zo ne a daidai lokacin da Habasha ke bikin murnar shiga sabuwar shekara.
A watan Mayun 1998 ne kasashen biyu suka fara yaki inda kowacensu ke kokarin kwace iyakar, inda hakan ya jawo mutuwar dubban mutane.
Yakin ya kare ne a shekarar 2000 bayan kasashen biyu sun kulla yarjejeniyar kawo karshen yakin.
Ita dai kasar Eritiriya ta kwaci ’yanci ne daga kasar Habasha a 1991.