Habasha ta naDa mata rabin ministocinta saboda ba sa cin hanci

A karon farko, Firayi Ministan Habasha Abiy Ahmed, ya naDa mata rabin ministocin Majalisar Zartarwarsa, ciki har da Ma’aikatar Tsaro. Da yake bayani kan matakin nasa ga ’yan majalisar dokoki, Mista Abiy ya ce mata ba su faye “cin hanci da rashawa kamar maza ba,” kuma za su taimaka wajen dawo da zaman lafiya da […]

Habasha ta naDa mata rabin ministocinta saboda ba sa cin hanci

A karon farko, Firayi Ministan Habasha Abiy Ahmed, ya naDa mata rabin ministocin Majalisar Zartarwarsa, ciki har da Ma’aikatar Tsaro.

Da yake bayani kan matakin nasa ga ’yan majalisar dokoki, Mista Abiy ya ce mata ba su faye “cin hanci da rashawa kamar maza ba,” kuma za su taimaka wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A yanzu Habasha ce kaDai kasar da take da wakilcin jinsi daidai a Majalisar Zartarwa a Afirka bayan Rwanda. Tun bayan zamowarsa Firayi Minista a watan Afrilu Abey Ahmed ya yi manyan sauye-sauye da dama.

Ya kawo karshen rikicin da aka shafe shekaru ana yi tsakanin kasarsa da makwabciyarta Eritireya, ya kuma saki dubban fursunonin siyasa tare da sassauta matsin da ake fama da shi a fannin tattalin arziki.

A’isha Mohammed ce ta zama Ministar Tsaron Habasha ta farko.

’Yar asalin yankin Afar da ke Arewa maso Gabashin kasar, ta kuma taBa rike Ministar Gine-Gine kamar yadda BBC ya ruwaito.

Muferiat Kamil wadda tsohuwar Shugabar Majalisar Kasar ce ta zama Ministar Zaman Lafiya.

Mahlet Hailu, wanda shi ne Matamakin Wakilin Dindindin na kasar a Majalisar Dinkin Duniya, ya wallafa jerin sunayen sababbin ministocin a shafinsa na Twitter

Firayi Ministan ya ce mata sun bayar da gagarumar gudunmawa wajen dawo da zaman lafiya, kuma ba su faye cin hanci ba, sannan suna girmama aikinsu kuma za su iya daurewa wajen kawo sauyi.

A watan Afrilu  Mista Abiy mai shekara 42 ya zama Firayi Minista bayan da Hailemariam Desalegn ya yi murabus Din ba-zata.