Hada kai shi ne karfi
Bisa ga dukkan alamu hatsaniyar da ta gauraye Majalisar Dattijai sakamakon zaben Shugabanninta ta kwaranye bayan jam’iyyar APC mai rinjaye a cikinta ta canja matsayinta na kin amincewa da wadanda aka firfitar a matsayin sabbin shugabanni bisa zargin cewa an ci amanarta, an kuma karya ka’idojin Majalisar na gudanar da zabubbukan Shugaba da mataimakinsa yadda […]
Bisa ga dukkan alamu hatsaniyar da ta gauraye Majalisar Dattijai sakamakon zaben Shugabanninta ta kwaranye bayan jam’iyyar APC mai rinjaye a cikinta ta canja matsayinta na kin amincewa da wadanda aka firfitar a matsayin sabbin shugabanni bisa zargin cewa an ci amanarta, an kuma karya ka’idojin Majalisar na gudanar da zabubbukan Shugaba da mataimakinsa yadda ya kamata. Wannan al’amari shi ne mafi a’ala ga jam’iyyar da kuma ita Majalisar Dattijai har ma da kasar baki daya. Domin kuwa rashin jituwar shugabannin Majalisar da kuma na jam’iyyar APC abu ne da zai iya kawo cikas wajen gudanar da harkokin Majalisar har ma da wadanda suka shafi ciyar da kasa gaba. A tsari irin na Shugaba mai cikakken iko, bisa tafarkin dimokradiyya, wajibi ne ya samu kyakkyawar dangantaka tsakaninsa da Majalisar Dattijai da kuma ta Wakilai domin kuwa ta kansu ne zai bi ya aiwatar da ayyukansa. Majalisun Tarayya da kuma bangaren Shugaban kasa tamkar hannun dama ne da na hagu, kowane zai cuda dan’uwansa wajen tafiyar da al’amuran da ke gabansa.
Ashe kuwa idan haka ne babu ta yadda za a yi Shugaban kasa ko kuma shugabannin Majalisun tarayya su kasa fahimtar juna har sai ta kai babu wani hadin kai tsakaninsu, domin kuwa da zaran an kaddamar da Majalisa, ‘ya’yanta kuma sun fara tunkarar ayyukan da ke gabansu.To suna kawar da batutuwan siyasa ne daga cikin dukkan batutuwan da aka gabatar masu, su sanya kasar a gaba, su hada kai da baki wajen ganin sun yi abin da zai kawo ci gaba ga kowa da kowa ba wani bangare ko don amfanin wani jinsi ba. Wannan ne ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ya dage wajen ganin cewa shugabannin jam’iyyarsa ta APC sun girmama Majalisar kasa a matsayinta na mai cin gashin kanta, bisa hurumin da ya ba ta damar gudanar da al’amuranta daban daga na sauran bangarorin mulki ba tare da katsalandan daga kowace shiyya ba.
Shugaba Muhammadu Buhari ya fi kowa sanin cewa wajibi ne a ba ‘ya’yan majalisun daga jam’iyyun adawa damar tsoma bakunansu cikin harkokin da za a tattauna a cikin Majalisu, sa’annan kuma ya kwana da sanin cewa komin kyawunsa sai ya hada da wanka, domin ko da yake jam’iyarsa ce ke da rinjaye zai nemi taimako da agazawar ‘ya’yan jam’iyyun adawa don samun sukunin amincewa da batutuwa da shawarwari da kuma dokokin da zai gabatar gaban majalisa. Idan zai dogara ne kan ‘ya’yan jam’iyyarsa kadai a cikin majalisar, suna iya bijire masa a wasu lokutan, kuma tana iya yiwuwa ‘yan adawa ne za su dage don ganin lallai manufofi da shawarwarinsa sun yi tasiri a cikin majalisar, an kuma zartar da su yadda yake so. A harka ko kokarin kafa dokoki a majalisa ba a sanin maci tuwo sai miya ta kare.
Dangane da haka ana iya cewa tayar da hakarkarin da wasu ke yi, har suna kumfan baki cewa wai jam’iyyar PDP ta kwashe masu kafa a Majalisa kuskure ne babba, domin kuwa ai har yanzu dan jam’iyyar APC ne, watau Sanata Bukola Saraki ke shugabancin Majalisar kasa, kuma dan’uwansa ne, Rayit-Honorabil Yakubu Dogara, ke shugabantar Majalisar Wakilai. To ta ina ke nan za a iya cewa jam’iyyar PDP ce ke mulkin Majalisar kasa? Wasu na ganin cewa zamantowar dan jam’iyyar PDP, Senator Ike Ejweremadu wanda ya sake darewa kujerar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai a karo na uku al’amari ne da ake ganin zai ba jam’iyyarsa damar tsoma baki ko yin katsalandan a harkokin gudanar da harkoki ta yadda zai muzgunawa ‘ya’yan jam’iyyar APC,To ai wajibi ne ko Ike Ekweremadu na mataimakin shugaban Majalisa ko kuma a matsayin dattijon Majalisa, wanda bai rike da wani mukami, ya tsoma baki cikin dukkan harkokin da ke gudana cikin Majalisa, kuma tilas ne a yi da dukkan ‘ya’yan jam’iyyarsa da ke cikin Majalisar, domin kuwa ba ‘yan jam’iyya mai rinjaye ce ba kadai za su yi muhawara kan dukkan shawarwari da kudurorin da Shugaban kasa zai aiko da su Majalisar don neman amincewa kafin a fara aiki da su, ko a mayar da su doka.
Haka nan kuma akwai wasu da ke da’awar kyamar ‘ya’yan jam’iyyar PDP, manyansu da kananansu, wadanda suka rikide ‘yam’iyyar APC, walau bayan wanzuwarta, ko kuma tun kafin wasu jam’iyyu uku su narke, su zame abu guda. Irin wadannan mutanen suna nunawa irin wadancan mutanen iyakarsu, alhali kuwa sun yi ban-kwana da jam’iyyar PDP, sun kuma fi mai kora shafawa a jam’iyyar APC, hasali ma da bazarsu ce aka yi rawa har aka samu galba a zaben Shugaban kasa da na Gwamnoni a dukkan sassan tarayyar kasar nan. Shi ya sa ake tunasar da wadancan mutanen masu kyamar wadanda suke kira ‘yan PDP a cikin jam’iyyar APC, su san cewa a cikin jam’iyyarsu babu wani gefe, da bakon asubahi da na maraice duk daya ne a cikin jam’iyyar. Sa’anan kuma ko a addinin Musulumci ma an nuna cewa da wanda aka haifa a cikin Musulunci, da wanda ya ridda, ya komo cikin addinin bayan shekaru aru-aru yana bin wani addinin, dukkansu daya ne babu wanda ya fi sai wanda ya fi jin tsoron Allah. To wa ya sani ko su wadancan da ake gorantawa don sun taba zama ‘yan PDP sun fi kaunar jam’iyya da yi mata hidima? Ai idan ungulu ta biya bukata sai balbela ta tafi da farinta.
Da Majalisar kasa da bangaren zartarwa duk dodo guda suke yi wa hidima, cikinsu kuma ba wanda zai iya yin wani katabus ba tare da taimakon gudan ba. Shi ya sa ake fatan wanzuwar kyakkyawar dangantaka da hadin kai tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da kuma Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Bukola Saraki, domin ta haka ne za a fadi tare, a kuma tashi tare. Hada kai dai shi ne karfi.