Hada kan kasa: “Akwai jan aiki a gaban Tinubu”
Kafin Zaben Shugaban Kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, wanda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar da Bola Ahmed Tinubu na APC a matsayin wanda ya lashe, abubuwa da dama sun faru wadanda suka kara fito da rarrabuwar kawuna tsakanin ’yan Najeriya a fili. An dai samu rarrbuwar kawuna ta fuksar addini da kabilanci da […]
Kafin Zaben Shugaban Kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, wanda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar da Bola Ahmed Tinubu na APC a matsayin wanda ya lashe, abubuwa da dama sun faru wadanda suka kara fito da rarrabuwar kawuna tsakanin ’yan Najeriya a fili. An dai samu rarrbuwar kawuna ta fuksar addini da kabilanci da bangaranci sakamakon matakan da wasu jam’iyyu ko ’yan takara suka dauka ko suka kasa dauka. Yayin da ake Shirin rantsar da Tinubu ranar 29 ga watan Mayu, mun shirya kawo muku trahotanni na musamman a kan kalubalen da sabuwar gwamanti za ta fuskanta. A wannan rahoto na musamman za mu duba mu gani ko rarrabuwar kawunan da aka samu za ta yi tasiri a kan tafiyar da mulki; kuma ko Tinubu zai iya hada kan ’yan Najeriya?
Nan da ’yan kwanaki masu zuwa, wato ranar 29 ga watan Mayu 2023, za a rantsar da Bola Ahmed Tinbu a matsayin sabon Shugaban Najeriya.
Zai sha rantsuwar ne bayan ya lashe babban zaben da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu – zaben da aka kwashe tsawon shekaru ba a sami irinsa ba, inda wanda ya yi nasara ya lashe shi da kaso mafi karanci, tun bayan zaben shekarar 1979.
To sai dai masana harkokin siyasa da masu sharhi a kan al’amuran yau da kullum na cewa zaben ya zo ne a lokacin da kasar ke fama da kalubalen karancin hadin kan kasa ta bangaren addini da kabilanci da kuma bangaranci.
‘Tun bayan Yakin Basasa, Najeriya ba ta taba shiga irin wannan yanayin ba’
A cewar tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), kuma Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, rabon da Najeriya ta fuskanci irin wannan rarrabuwar kan tun zamanin Yakin Basasan da aka yi a shekarun 1969-1970.
Sanusi, wanda ya bayyana hakan yayin jawabinsa a wani Taron Kasa Kan Tattalin Arziki da Shugabanci don murnar cikar babban malamin addinin Kirista, Ituah Ighodalo, shekara 62 a duniya, ya ce sakamakon zaben da ya gabata, yanzu kasar ta dare gida biyu saboda bambance-bambancen addini da na kabilanci.
Ya ce, “Yanzu wannan matsalar ta jefa shakku a zukatan jama’a kan duk wata irin doka ko mataki da gwamnati za ta dauka bayan zabe.
“Wannan ne ma ya sa a watan Oktoban bara, a yayin Taron Zuba Jari na Jihar Kaduna, na shawarci ’yan Najeriya cewa duk wanda ya ce musu magance matsalolin Najeriya a 2023 abu ne mai sauki, kada su zabe shi, saboda bai san girman matsalar ba.
“Ba na tunanin kasar nan ta taba shiga halin tsaka mai wuya irin wannan tun bayan Yakin Basasa.
“Muna fuskantar kalubalen sake gina kasa. Bambance-bambancen addini da na kabilanci sun yi mana katutu, ga tattalin arzikinmu yana cikin tsaka mai wuya, sannan ga rarraunan shugabanci,” in ji Sanusi.
Sai dai masu sharhi kan al’amuran yau da kullum da shugabannin al’umma da sauran jagororin jam’iyyu suna ganin duk da wannan kalubalen na rarrabuwar kan ’yan kasa ta fuskar addini da kabilanci, sabon Shugaban Kasa zai iya dinke duk wata baraka idan ya dauke su a matsayin tsintsiya madaurinki daya.
A cewar Shugaban Jami’ar Tarayya da ke Kashere a Jihar Gombe, Farfesa Umar Pate, akwai dalilai na ciki da waje wadanda suka haddasa matsalolin, amma alhakin sake hade kan kasa na wuyan sabon shugaban.
Sai dai shehun malamin ya ce duk da cewar kantafin da aka yi da amanar al’umma ne musabbabin matsalolin da kasar ke ciki, wadanda suka haddasa kashe-kashe da lalata dukiyoyi da ma yunkurin ballewa daga kasa, akwai jan aiki wajen tabbatar da ci gaba da kasancewar Najeriya kasa daya.
Ya ce, “Idan ka kalli Kundin Tsarin Mulkinmu da ma tsarin siyasarmu, duka za ka ga an tsara su ne ta yadda za su ba kowa damar da zai ji ana damawa da shi.
“Shawarata ga gwamnati mai zuwa ita ce ta kalli Najeriya a matsayin kasa daya. Ta duba wasu tsare-tsaren da aka bi a baya (na hada kan kasa) har aka zo inda ake yanzu.
“Magana ce ta tafiya da kowa ba tare da nuna bambanci ba, ta samar da dimokuradiyyar da za ta sa kowa ya ga dalilin ci gaba da zamansa a kasar, ba yin abun da da gangan zai yi wa tsarin zaman tare zagon kasa ba,” in ji malamin.
Kalaman kiyayya da kin jinin juna
Shi ma wani fitaccen masanin harkar tsaro da leken asiri, Dokta Kabiru Adamu, ya jaddada cewa zargin nuna bambanci da wasu al’ummomi da wasu yankunan kasar nan ke yi wa gwamnati sun taka muhimmiyar rawa wajen sake rura wutar.
Kodayake ya ce sakamakon zaben 2023 ya nuna karara yadda manyan ’yan takara suka yi amfani da bambance-bambancen addini da kabila wajen cim ma bukatunsu na kashin kai, yadda dan takarar PDP, Atiku Abubakar da takwaransa na jam’iyyar LP, Peter Obi suka koma kotun sauraren kararrakin zabe don neman bahasi ya yayyafa wa wutar ruwa.
Ya ce, “Batutuwan da suka dabaibaye zaben 2023 da irin rawar da kusan dukkan manyan ’yan takara uku a zaben suka taka, da kuma yadda aka rika yada kalaman kiyayya da na kin jinin juna a lokacin zaben, duk sun taka mummunar rawa a zaben da kuma sakamakonsa,” in ji shi.
Dangane da hanyar da ya kamata a bi wajen magance wadannan matsalolin, masanin, wanda kuma shi ne Shugaban kamfanin Beacon Consulting Limited, ya kara da cewa, “ya kamata gwamnati mai jiran gado ta fito da nagartattun tsare-tsare da za su sake hada kan kasa, su tabbatar da adalci da daidaito da janyo kowa a jika, ta yadda kowanne bangare na kasar zai rika jin ana tafiya tare da shi”.
Abin da ya wajabta a yi
Shi ma wani lauya masanin Tsarin Mulki, Kayode Ajulo, ya ce Tinubu na da jan aiki a gabansa wajen sake hada kan kasar da magance kalubalen tsaro da kuma samar da ayyukan more rayuwa da kuma bunkasa tattalin arziki.
Shi ma Farfesa Pate ya kara da cewa baya ga magance wadannan matsalolin, ya zama wajibi sabuwar gwamnati ta magance matsalar cin hanci da rashawa wadda ya ce tana cikin manyan matsalolin da ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya.
Ya ce matukar ’yan Najeriya suka fahimci tana da kyakkyawar aniya ta mutunta su ba tare da nuna bambanci ba, za su ba shi cikakken hadin kai.
“Ina fatan gwamnatin za ta mayar da hankali wajen magance rashawa da samar da ayyukan raya kasa da inganta ilimi da bangaren aikin gwamnati da adalci, kamar yadda dokokin kasa suka tanada wajen tsarin raba-daidai,” in ji Farfesa Pate.
Shi ma Dokta Kabiru Adamu ya shawarci sabuwar gwamnatin da kada ta yi wa tsarin shari’ar zaben da yanzu haka ake gudanarwa katsa-landan, ta yadda za a ga kotunan a matsayin masu cin gashin kansu.
Rinjaye mafi karanci
Shi kuwa shugaban makarantar Development Specs Academy, Farfesa Okey Ikechukwu, shawartar dukkan masu ruwa da tsaki ya yi, musamman ma masu neman hakkokinsu a kotu, da su mutunta kowanne irin hukunci kotunan za su yanke a kan kararrakinsu na zabe.
Ya ce kodayake Tinubu ya lashe zaben ne da kuri’u mafiya kankanta tun bayan dawowar Najeriya mulkin Dimokuradiyya a 1999, hakan ba zai kawo masa wani tasgaro ba, tun da dai ya cika dukkan sharuddan da doka ta tanada kafin lashe zabe na samun kuri’u mafi rinjaye kuma a sassa daban-daban na fadin kasar.
Sai dai ya ce akwai barazanar samun karuwar rarrabuwar kai a fafutukar rabon mukamai, kamar yadda ake gani a wajen neman shugabancin Majalisun Tarayya.
“Rarrabuwar kan na dada karuwa yayin da ake ci gaba da kokawar neman mukamai, amma ina fatan abubuwa za su inganta, da zarar Shugaban Kasa ya daidaita a kan mulki kuma ya rungumi kowa hannu bibbiyu.
“Ina kuma son Shugaban ya kyale ’yan Najeriya, musamman ma ’yan siyasa, su fahimci cewa ba mu da wata kasar da ta wuce Najeriya, ballantana mu yi tunanin lalata ta,” in ji shi.
Shugaban jam’iyyar APC a Jihar Legas, Cornelius Ojelabi, ya ce yana da yakinin babu makawa gwamnatin Tinubu za ta hada kan ’yan Najeriya.
“Ba a kai ga rantsar da shi ba tukuna, amma idan aka yi la’akari da abubuwan da ya yi a baya, muna kyautata masa zaton zai kara hada kai da kuma ciyar da kasar gaba.
“’Yan Najeriya su kara hakuri har a rantsar da shi tukunna, za su ga kyawawan manufofinsa sun fara aiki gadan-gadan,” in ji Shugaban na APC.
To sai dai masu magana da yawun PDP da wakilinmu ya bukaci jin ta-bakinsu sun ki su ce uffan, suna cewa ba abin da za su ce a kan gwamnatin har sai kotu ta yanke hukunci kan karar da suka shigar suna kalubalantar zaben Tinubu.
Sakataren Yada Labarai na PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya ce har yanzu maganar sahihancin zaben Tinubu na gaban kotu.
Shi ma wanda ya gabace shi a kan kujerar, kuma Kakakin Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar a zaben 2023, Kola Ologbondiyan, ya ce, “PDP tare da dan takararta na Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, yanzu haka suna gaban kotu kan zaben. Don haka ba zan ce komai ba a kai har sai an yanke hukunci”.
Kazalika, daya daga cikin masu magana da yawun kwamitin yakin neman zaben na Atiku, Charles Aniagwu, wanda kuma shi ne Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Delta, shi ma ya ki cewa uffan a kai.