Hadaddiyar kungiyar matasa ta yi gangamin tsaftace muhalli a Sabo Ibadan
Hadaddiyar kungiyar matasa ta Arewa Youth Forum (AYF) a Jihar Oyo da hadin guiwar sashen bunkasa kiwon lafiya da ilmi na Kwalejin Magani a Jami’ar Ibadan, sun yi wani gangami, a ranar Lahadi domin tsaftace muhalli a unguwar Sabo Ibadan. Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ahmad dahiru Zungeru da Sarkin Barebarin Ibadan, Alhaji Babagana Alhaji Kyari […]

Hadaddiyar kungiyar matasa ta Arewa Youth Forum (AYF) a Jihar Oyo da hadin guiwar sashen bunkasa kiwon lafiya da ilmi na Kwalejin Magani a Jami’ar Ibadan, sun yi wani gangami, a ranar Lahadi domin tsaftace muhalli a unguwar Sabo Ibadan.
Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ahmad dahiru Zungeru da Sarkin Barebarin Ibadan, Alhaji Babagana Alhaji Kyari da Shugaban kungiyar Arewa Youth Forum, (AYF) Alhaji Abubakar Tijjani, su ne suka jagoranci tsaftace muhallin a cikin lungunan unguwar, inda aka share kazanta daga cikin kwatami da kuma kwashe bola.
kungiyoyi 3 na matasan unguwar, Sabo Youth Alliance da Amana Youth Association da Sabo Students Progressibe Union su ne suka dunkule suka samar da gamayyar kungiyar matasan Arewa Youth Forum (AYF), wacce ta fara gudanar da babban taronta na farko a ranar Asabar, a inda aka yanke shawarar gudanar da gangamin tsaftace muhallin a ranar Lahadi.
Mista John Imaledo, na sashen kiwon lafiya da ilmi a Jami’ar Ibadan shi ne ya jagoranci wasu jami’an duba gari zuwa wajen babban taron da gangamin tsaftace muhallin.
Cikin jawabin da ya yi wa daruruwan matasan, Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ahmad dahiru Zungeru ya nemi jama’a masu hannu da shuni su taimaka wa kungiyar da kudaden sayen kayan aiki kuma su rika fitowa ana gudanar da irin wannan muhimmin aiki da su. “Wannan zai karfafa wa ’ya’yan kungiyar guiwar ci gaba da ayyukan sadaukar da kai da suka fara daga cikin aljihunsu ba tare da sun nemi gudunmawa daga waje ba.” Inji shi.
Shi kuwa Sarkin Barebarin Ibadan, Alhaji Babagana Alhaji Kyari jinjina wa matasan ya yi da cewa, “Tarihi ba zai taba mantawa da irin wannan yunkuri da kungiyar matasan (AYF) ta gudanar a cikin unguwar Sabo ba, musamman domin sun fito da wani muhimmin abu ne da zai taimaki dubunnan al’ummar Arewa da ke zaune da iyalinsu wajen maida hankalin kan lamarin tsaftace muhalli. Ba a taba samun kungiyar da ta gudanar da irin wannan gagarumin shiri a baya ba. Saboda haka ya kamata mu yi dukkan abun da muke iyawa wajen tallafa wa kungiyar, musamman ta fannin daukar nauyin samar mata babban ofishin da za su rika gudanar da harkokinsu.”
Tun farko a cikin jawabinsa, Shugaban Gamayyar kungiyar, Alhaji Abubakar Tijjani ya karanto muhimman abubuwa guda 4 ne a matsayin manufofin kungiyar. “Wadannan abubuwa su ne, tabbatar da hadin kan dukkan ’yan Arewa da ke zaune a jihohi 6 na yammacin kasa; da taimaka wa irin wadannan mutane wajen magance irin matsalolin zamantakewa da suke fuskanta ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba; da taimako na musamman ga makarantun Islamiyya da masallatai da makabartu da ziyartar gidajen marayu da asibitoci; da kuma kula da tarbiyyar yara da tsaftace muhalli, wanda muka fara da shi a yanzu. Mun tsayar da ranar Lahadin karshen kowane wata ta zama ranar sharar unguwarmu domin tsaftace muhallanmu da zai kawar da mu daga kamuwa da cutuka da suke yaduwa a dalilin kazanta”.
Daga nan sai ya nemi hadin kan jama’a, musamman iyaye, su rika yin nasiha ga mata da kananan yara a game da illar zama a cikin kazanta, musamman ganin gwamnati ta wadata garin da motocin kwashe shara, “Saboda haka ya kamata mu ma mu shiga cikin shirin tsaftace muhalli domin amfanin kanmu”. Inji shi.
Matan aure da ke cikin gida, don bayar da tasu gudunmawar, sun yi ta aikawa da ruwan sha da sabulu da tsintsiyar shara da magungunan kashe kwari da aka yi amfani da su wajen kammala aikin sharar.
Gangamin tsaftace muhallin, wanda aka yi awoyi 6 ana gudanarwa ya ga jama’a daban-daban da suka hada da Sarkin Hausawa da Sarkin Barebari da Dattijo Alhaji Umba Bawa, wadanda suka sanya kananan riguna suka dauki manjagara da shebur suka rika shiga cikin kwalbatoci domin yasar tulin kazanta duk don a samu a tsaftace muhalli, sauran jama’a suna kwasa suna zubawa cikin manyan motocin kwasar sharar da aka giggirke. Su kuma jami’an duba gari suna bi suna feshin magunguna.