Hadakar Kungiyar Dattawan APC sun goyi bayan Buhari a 2019

Kungiyar Dattawan APC na Arewa maso Yamma sun nuna goyan bayansu ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019. Don karasa muhimman ayyukan raya kasa da ci gaban da ya faro fiye da shekaru uku da suka gabata. Shugaban Kungiyar na Jihar Kebbi, Alhaji Sani Zauro Hukuma (Zannan Gwandu) shi ne ya bayyana haka ga […]

Hadakar Kungiyar Dattawan APC sun goyi bayan Buhari a 2019

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Kungiyar Dattawan APC na Arewa maso Yamma sun nuna goyan bayansu ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019. Don karasa muhimman ayyukan raya kasa da ci gaban da ya faro fiye da shekaru uku da suka gabata.

Shugaban Kungiyar na Jihar Kebbi, Alhaji Sani Zauro Hukuma (Zannan Gwandu) shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a ofishinsa dake Birnin Kebbi. Yana mai cewa babu wani dan takara a Najeriya da za a iya kwatanta kimarsa da ta Buhari, don haka yake fatan ‘yan Najeriya su bashi goyon baya karo na biyu don karasa fitar da kasar nan daga bala’in da ya same ta tsawon shekaru.

A cikin wadannan shekaru uku da ‘yan watanni na Buhari, ya nuna wa duniya cewa shi gwarzo ne kuma adalin shugaba, wanda yake aikata dukkan abinda ya fada. Kuma kyawawan ayyukansa ne suka sanya mu dattawan APC na yankin Arewa maso Yamma dake cikin wannan kungiya dan ba shi goyon.

“Dukkan dan Najeriya nagari zai goyi bayan Shugaba Buhari, domin ba kansa da iyalansa ne gabansa ba, kasar ce a gabansa. Kuma kafin zuwan Buhari komai a kasar nan ya lalace. Tabarbarewar tattalin arzikin kasa da tsaro, sannan da tsananin cin hanci da rashawa da ya mamaye kusan dukkan ma’aikatun gwamnati. Amma daga hawansa ya saita komai yadda ya kamata,” inji shi.

 

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa