Hadamar abinci
Wani Inyamiri ne ya je kasar Hausa sai aka hada su cin abinci tare da gardawa, to kuma ga abincin da zafi. Kun san gardi, ba ruwansa da zafi, kafin Inyamiri ya yi loma daya, gardawa sun yi uku-uku. Daga can sai wani ya ce: “Kai, ai kuwa Manzon Allah ya hana cin abinci da […]
Wani Inyamiri ne ya je kasar Hausa sai aka hada su cin abinci tare da gardawa, to kuma ga abincin da zafi. Kun san gardi, ba ruwansa da zafi, kafin Inyamiri ya yi loma daya, gardawa sun yi uku-uku. Daga can sai wani ya ce: “Kai, ai kuwa Manzon Allah ya hana cin abinci da zafi.” Jin haka sai Inyamiri yi zumbur ya ce: “Kai, ai kuwa ya Kyauta!
Daga Idris Gagare Rurum 08023866232