Hadari a kan hanyoyinmu: Laifin wa?

A wannan makon, mun samu wannan tsokaci mai take na sama, daga kwararren malamin asibiti ta bangaren jinyar kashi, MALAM IS’HAKA SARKIN FULANI DANKAMA (08100006858): Hatsari, kalma ce da ake alakanta ta da wani al’amari da ke faruwa ya haifar da jin rauni ko nakasa ga wani abu mai rai ko maras rai, ko kuma […]

Hadari a kan hanyoyinmu: Laifin wa?

A wannan makon, mun samu wannan tsokaci mai take na sama, daga kwararren malamin asibiti ta bangaren jinyar kashi, MALAM IS’HAKA SARKIN FULANI DANKAMA (08100006858):

Hatsari, kalma ce da ake alakanta ta da wani al’amari da ke faruwa ya haifar da jin rauni ko nakasa ga wani abu mai rai ko maras rai, ko kuma salwantar da dukiya ko rai.
Hatsari al’amari ne da ka iya zama na ba-zata, ba tare da masaniyar faruwarsa ba kuma da wahala a kare faruwarsa ko a lokacin da yake faruwa, kasancewar ya auku ba a cikin shiri ba, haka kwatsam.
Duk da haka, bincike ya nuna cewa wasu lokuta za a ga alama ko zaton faruwar hatsarin dangane da rashin kiyaye dokoki na kare wannan dukiya ko rai. A takaice dai hatsari tsautsayi ne da ka iya haddasa asara ta lafiya ko ta dukiya ko ma ta rai.
Hatsari wani bangare ne da ake samun karancin kulawa daga gwamnati, idan aka yi la’akari da sauran nau’o’in rashin lafiya. A Kullum ana samun sauye- sauye kamar yadda kungiyoyin Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana a takenta ‘Lafiya Ga Kowa A Shekarar 2000’ musamman ikirarinta na cawa za a samu raguwar hatsari kashi 25 zuwa 30 cikin dari da yawan rasa rayuka a kasashen Turai da Afrika.
kungiyar Lafiya ta Duniya ta kara da yin gargadi da ba da shawara da kuma yin hannunka-mai-sanda, cewa idan mutane daidaiku da kungiyoyin da ba na gwamnati ba da gwamnatoci a kowane mataki sun raja’a da tsunduma sosai wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, ba ta hanyar kare aukuwar hatsari a kasashen Afrika, babu makawa ko kokwanto a kan hanya da rasa rayuka na nakasa zuwa shekara ta 2020, a maimakon matsayi na tara da yake a yanzu, zai dawo matsayi na uku.
Nau’o’in Hatsari: Hatsari kamar yadda aka yi bayaninsa a baya, akwai nau’o’innsa daban-daban:
1-Hatsarin hanya: Wannan shi ne nau’in hatsari da mutanen duniya musamman a kasashen Afrika suka aminta da shi ne hatsarin da yake faruwa fiye da kowane nau’i a hatsari. A sanadinsa akan yi asarar dukiya ko wani sashe na jiki ko ma a rasa mutane ko dabbobi ko abin hawa.
2-Hatsarin sana’ar hannu (karfi): Sana’o’in hannu, musamman na Hausawa, akan iya samun hatsari a yayin aiwatar da su. A wannan lokacin hatsarin sai ya dawo doron kasa ba cikin shiri ba. Hatsari na sana’ar hannu ya hada da irin yadda mutane ke hawa saman itaciya, ko gini, ko shiga cikin rami kasa, wanda yakan kawo nakasa a jiki ko ma rasa ran masu sana’ar.
3-Hatsarin masaka da kamfanoni: Hatsari yakan auku a masaka da kamfononi a dalilin illar da abubuwan injinan da ake amfani da su suke fitarwa da ma’aikatan kan shaka. Ire-iren wadannan sun hada da iskar ko gari kan wannan sinadarai da ake sarrafawa don samar da abubuwan da ake, misali yadi ko atamfa ko siminti ko magani da sauransu. Yawan shakar sinadarin ruwan gas ko kurar siminti, fulawa, dusar katako da makamantansu kan haddasa hatsarin kamuwa da cututtuka irinsu lamoniya da asma. Hatsari na nakasar fatar jiki, ko wani bangare na jiki, sanadiyyar yawan zubar sinadirin da ake amfani da shi a masaka ko wani kamfani ga jikin mutum. Hatsari na nakasar da gani ko makancewa sanadiyyar hasken lantarki ko yawan duhu da masaka ko kamfanoni suke amfani da su. Hatsari na nakasar da ji ko kurumcewa, sanadiyyar yawan jin karar injina. Rauni ko gocewa ko targade ko karayar kashi, sanadiyyar bugewa ko lalacewar injin lantarki, ko wayoyin lantarki.
4-Hatsari na gida.
5-Hatsari ta hanyar yin wasanni.
6-konewa ko salewa.
8-Hatsari ga yara: Rashin kulawa ko sakaci, musamman na iyaye mata da suke zaune a gida tare da ’ya’yansu yakan haddasa aukuwar hatsari ga yaran. Wannan yakan faru musamman ga yara ’yan shekara daya zuwa biyar da haihuwa. Sau da yawa akan sami yaro ya sha kalanzir ko fetur ko ya sha magani cikin kwalba ko ya taune kwayoyin magani ya hadiye da sauransu.
Abubuwan da ke haddasa hatsari a hanya: Al’amurra da dama suna faruwa wadanda kuma suke zama sanadiyyar hatsari. Wadannan dalilai suna da tarin yawa, don haka a nan za a kawo wasu daga cikinsu kamar haka:
Rashin kyan hanya: Yayin da ya kasance hukuma wadda hakkinta ne ta gina wa jama’arta hanyoyi ba ta gina ba, ko kuma ta gina ba ta inganta su ba, to ba wani kokwanto hakan ka iya zama dalilin da ka haddasa aukuwar hatsari ga masu abin hawa da mutane da dukiyar da suke a kan wannan abin hawan. Rashin kyan hanya ya hada da rashin wurin sauna na gefen hanya (shoulder), rashin alamomi na kan titi, rashin alamomi na gefen titi, watau irin allon nan da ke nuna akwai kwana, ko akwai gada da sauransu. Rashin wurin tsayawa da mota, domin sauke ko daukar fasinjan ko kaya a garuruwan da suke kan hanya. Matsattsa ko gajeruwar kwana, gada maras fadi, mai hannu daya, yawan ramuka a kan hanya da yawan hawa ko gangara a kan hanya.
Munanan dabi’u na direbobi: A lokuta da dama akan samu masu abin hawa suna aiwatar da munanan dabi’u yayin da suke kan abin hawa. Haka kuwa na faruwa bisa dalilai daban-daban da suka hada da ganin sun fi karfin doka ko babu dokar, ko da akwai dokar ba a, ko kuma izgilanci, ko jahilci, ko ganganci, ko burgewa ko gwaninta. Ko ma mene ne dalili, munanan dabi’un direbobi suna yin sanadiyyar aukuwar hadurra, wadanda sukan yi sanadiyyar asarar rayuka, wani lokaci har da nasu direbobin, da lafiya, da dukiyar al’ummar da ba a san adadi ba.
Ire-iren wadannan dabi’u sun hada da shan kayan maye (giya ko tabar wiwi), karin lokacin da ake yin tuki, gudu da abin hawa da wuce kima, tsayawa da mota rabin jikinta na kan hanya, musamman domin dauka ko ajiye kaya ko mutane. Jahilta ko rashin sanin dokokin tuki, rashin lafiyar idon direba, rashin lafiyar kunne ga direba da tuki cikin halin damuwa, ko bakin ciki, ko rashin hankali na direba. Kunna dogon hasken fitilar mota ba lokacin da ya dace ba, ko kara fitilu ga mota. Yin waya, ko amsa wayar tafi-da-gidanka a lokacin tuki, tukin yara masu karancin shekaru (kasa da shekaru 18), tukin nakasassu (guragu da kurame). Tukin masu lalurar rashin lafiya kamar farfadiya, yawan jiki da ciwon sukari.
Za mu ci gaba