Hadari ne a bar mutanen da suka san yadda ake sarrafa makamai babu aikin yi – Janar MD Isa

Manjo Janar Mohammed danhanne Isah (mai ritaya) tsohon Kwamandan Kwalejin Horar da Manyan Hafsoshin Sojin Najeriya ce (ICS) da ke Jaji a Jihar Kaduna. A tattaunawarsa da Aminiya ya ce, idan ana son dakile Boko Haram da sauran ayyukan ta’adda to a koya wa matasan Arewa sana’o’i, domin bai kamata a bar wanda ya iya […]

Hadari ne a bar mutanen da suka san yadda ake sarrafa makamai babu aikin yi – Janar MD Isa

Manjo Janar Mohammed danhanne Isah (mai ritaya) tsohon Kwamandan Kwalejin Horar da Manyan Hafsoshin Sojin Najeriya ce (ICS) da ke Jaji a Jihar Kaduna. A tattaunawarsa da Aminiya ya ce, idan ana son dakile Boko Haram da sauran ayyukan ta’adda to a koya wa matasan Arewa sana’o’i, domin bai kamata a bar wanda ya iya sarrafa bindiga yana zaman kashe wando ba:

Aminiya: Kasancewarka masanin tsaro yaya kake ganin za a yi da matasa ’yan Boko Haram da suka ajiye makamansu?
Janar Isah: Tuntuni Najeriya na da shirin sauya hali da daidaitawa da kuma tsugunar da jama’a, don haka ya kamata a yi la’akari da yadda Janar Antonio Penula na Portugal ya yi, lokacin da yake yaki da ’yan tawaye masu neman ’yanci a kasar Guinea a shekarun 1970. Ya yi dabarar jan hankalin jama’a ne ta hanyar daina yaki da jirgi mai saukar ungulu, inda ya koma gina makarantu da asibitoci da ba da abinci don jama’a, su ba da asirin ’yan tawaye. Ya kamata a koya wa matasa yadda za su rayu cikin jama’a, don yakin sari-ka-noke ya kare, sai dai ’yan daidaikun da ba za a rasa ba a kauyuka. Kuma ina kira ga wadanda suka rage su a jiye mamakai su mika wuya, kafin a cin musu. Bugu da kari, su ma ’yan gudun hijira kada a bar su a baya, a koya musu sana’o’i. Kuma wadanda yakin ya shafa, kada su yi kasa a gwiwa, su ci gaba da neman na sawa a bakin salati, kuma su ja wadansua  jiki, su koya musu sana’o’in da suka iya kamar kanikanci da walda da tukin mota da gyaran kayan lantarki da fenti da gini da sauransu.
Aminiya: Wace gudunmuwa jama’a za su bayar don samar da zaman lafiya a Najeriya?
Janar Isah: Jama’ar Najeriya su tallafa wa wadanda yakin ya shafa, sannan su tona duk wani dan Boko Haram da ya tsere daga dajin Sambisa, ya yi shigar burtu ya shigo gari. Ya kuma dace jama’a su kula da tarbiyyar ’ya’yansu domin kada su yi cudanya da batagari saboda kada su saka su a cikin mugun aiki. Kuma masu aikin damara su kula kada su hada masu laifi da wadanda suke sababbin kamu wuri guda, domin kada su kara ingiza yara su zama manyan miyagu ko a chaji ofis, ko a wurin tsare mutane ko a gidan yari. Su kuma wadanda suka mika wuya suka ajiye makami tun kafin a ci karfinsu, kada jama’a su fada musu don daukar fansa, a yafe domin kada abin ya koma danye. Ina ba da shawara ga wadanda aka kama su sauya hali, su zamo masu bin doka sau da kafa.
Aminiya: Wane irin salon yaki Boko Haram suke yi?
Janar Isah: Boko Haram ba ’yan ta da kayar baya ba ne ingantattu, domin ba su samu goyon bayan jama’an kasar nan ba. Jama’a na goyon bayan Gwamnatin Tarayya ne. Kuma kasashe makwabta kamar Chadi da Nijar da Kamaru da Benin suna tare da Rundunar Hadin Gwiwa (MNJTF), kuma matasa ’yan sa kai wato (Sibiliyan JTF) sun yi rawar gani da sauran masu damara na yankin wadanda suka yi murabus duk sun ba da gudunmuwa.
Aminiya: Mene ne sirrin da ya sa sojoji suka yi rawar gani, ko don Shugaba Buhari ya ce su kawo karshen Boko Haram ne kafin karshen bara?
Janar Isah: Janar Buhari nemiji ne wanda ya yi tsayuwar daka irin na Sarkin Yaki dan Waire da Jan Gwarzo domin ya yi yaki kuma ya san zaman lafiyan kasa ya fi fada, bai ja da baya, don haka ne ya ce ‘Mene ne Boko Haram?.’ Saboda haka ne ya nada ’ya’yan yankin don su yi maganin abin da kansu, kamar Janar Monguno da Janar Tukur Buratai da Iya Mashal Siddikue Abubakar.
Aminiya: Mene abin da soja ya kamata su kula da shi?
Janar Isah: Soja da sauran jami’a tsaro su kula cewa, ’yan Boko Haram tsirarru suna yin amfani da yara kanana da aka sauya wa tunani don kai harin kunar bakin wake. Su kuma jama’a ya kamata su san cewa ba addinin da ya yarda da kunar bakin wake don kashe jama’a. Ya kamata jama’a su ci gaba da ba gwamnati goyon baya domin ci ci moriyar zaman lafiya ta hanyar bin doka da oda da kula da bakin ido, batagari don kada su cutar da bayin Allah ba gaira ba dalili.
Aminiya: Kana da kira ga masu wa’azin addini, Musulmi da Kirista?
Janar Isah: Ya dace a samar da malaman addinin Musulunci da fastoci na addinin Kirista da masu sanin halayen jama’a domin su yi wa’azi da jan hankali ga wadanda abin ya shafa, kan su mayar da komai ga Allah su zauna lafiya. Kuma ya dace a rika tantance masu yin wa’azi, ya zamo sai an tantance mutum kafin ya samu izini daga Jama’atu ko CAN, sannan su yi wa’azi dangane da yafiya da neman na kai, ba kowa ya zo ya yi wa’azin da bai dace ba.