Hadari ne Shugaba Jonathan ya ziyarci Chibok – Tanko Yakasai

Daya daga cikin dattawan Arewa Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana dalilan da suka hana Shugaban kasa Goodluck Jonathan zuwa garin Chibok da ke Jihar Borno inda aka sace ’yan mata sama da 200 watanni shida saboda suka gabata, inda ya ce akwai hadari a tattare da yin hakan.Alhaji Tanko Yakasai ya ce hadari ne babba […]

Hadari ne Shugaba Jonathan ya ziyarci Chibok – Tanko Yakasai
Hadari ne Shugaba Jonathan ya ziyarci Chibok – Tanko Yakasai

Daya daga cikin dattawan Arewa Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana dalilan da suka hana Shugaban kasa Goodluck Jonathan zuwa garin Chibok da ke Jihar Borno inda aka sace ’yan mata sama da 200 watanni shida saboda suka gabata, inda ya ce akwai hadari a tattare da yin hakan.
Alhaji Tanko Yakasai ya ce hadari ne babba a ce Shugaban kasa ya ziyarci yankin a wannan lokaci da abin ya faru domin a cewarsa komai na iya faruwa da Shugaban kasar idan ya ziyarci yankin wanda ke fama da rikici.
Alhaji Tanko Yakasai wanda ya bayyana haka a cikin shirin “Hannu da Yawa” da ake gabatarwa a gidan Rediyon Tarayya na Kaduna, ya kara da cewa akwai bukatar jama’a su rika hangen nesa a duk abin da suke yi.
Ya ce shi yana matukar jin tsoro a ce Shugaban kasa Jonathan ya ziyarci Chibok saboda lalacewar matakan tsaro a Arewa maso Gabas. Ya ce, “Komai za a yi, ya kamata a rika yi ana hangen nesa. Shugaban kasa ba soja ba ne, in da a ce ina Shugaban kasa, idan fitina irin wannan ta faru abin da zan yi shi ne in kai soja, in na kai su, su yi iyaka kokarinsu. Kuma sojan nan, ni a ra’ayina suna iyakacin kokarinsu, domin muna ji ana kashe su, kana ji, ina ji, ana fada a rediyo, ana fada a jarida. Kuma ban san abin da ya sa ba, ko bisa tsautsayi ne, babban mai ba shi shawara kan harkar tsaro dan Arewa ne, danmu ne, Ministan tsaro danmu ne, babban shugaban ’yan sanda, danmu ne dan Arewa, babban hafsan tsaro, dan Arewa ne, duk sojojin Najeriya a karkashinsa suke. To in duk wadannan ba su iya yi ba, Shugaban kasa shi kadai zai iya yi, anya kuwa zai iya?”
Saboda haka sai ya ce a tunaninsa rashin zuwan Shugaban kasa Chibok yana bisa kan ka’ida domin kauce wa abin da ka iya faruwa. “Idan ya tafi Chibok ya zama wadannan mutane da suka kware wajen kunar bakin wake, suka yi masa kwanton bauna, wani abu ya faru da shi fa, ana tsammanin mutanensa za su hakura ne?,” inji shi.
Alhaji Tanko Yakasai ya ce yanzu da aka bari rikicin yankin ya zama ruwan dare dole sai an yi shiri kafin a yi maganin matsalar, domin abin ya yadu fiye da yadda ake tsammani.
“Abin har ya kai yarinya ’yar shekara goma sha, za ta yi kundunbala, ta je a ba ta bom ta daura ta tayar da shi ya kashe mutane. To ka ga sanadiyyar yaduwar wannan fitina ke nan. Shi ya sa ake son a kashe fitina tun ba ta girma ba,” inji shi.
Ya ce bai ce ba dattawa daga Jihar Borno su nemi a janye sojoji daga jihohin da ake samun wannan tashin-tashina.
“Abin da ya gagari dan sanda, ya sa Gwamna ya roki Shugaban kasa ya kawo soja, aka kawo soja ya fitini sojan, don Allah akwai hankali a ce a kwashe sojan, kai kuma ba ka kawo wani abin da za a sa a madadin sojan ba?” Ya yi tambaya.
Ya roki jama’a su ci gaba da ba gwamnati shawarar hanyoyin da za a kawo karshen wannan fitina ya kuma nemi Musulmi da Kirista su ci gaba da yin addu’o’i domin samun zaman lafiya a kasar nan.