Hadarin da ke cikin zaben ashararai da wawaye a matsayin shugabanni (1)
Huduba ta Farko:Hamdala da taslimi: Bayan haka, ya ku bayin Allah! Lallai ina yi muku wasiyya da ni kaina da jin tsoron Allah (SWT), domin babu tsira a nan duniya da kuma Lahira, sai da tsoron Allah, kuma tsoron Allah shicne tushen dukkan alheran duniya da Lahira.Ya ku’yan Najeriya! Lallai idan za ku iya tunawa, […]
Huduba ta Farko:
Hamdala da taslimi:
Bayan haka, ya ku bayin Allah! Lallai ina yi muku wasiyya da ni kaina da jin tsoron Allah (SWT), domin babu tsira a nan duniya da kuma Lahira, sai da tsoron Allah, kuma tsoron Allah shicne tushen dukkan alheran duniya da Lahira.
Ya ku’yan Najeriya! Lallai idan za ku iya tunawa, a kan wannan mumbari mai albarka an sha jawo hankalinku a kan al’amarin shugabanci da hadarinsa da kuma muhimmancin zaben mutanen kirki, masu amana, masu kishin talakawa a kan shugabanci. To, har yanzu in Allah Ya so ba za mu gajiya ba, da yardar Allah za mu ci gaba da bayani, a ko’ina muka samu kanmu domin wayar da kan al’umma a kan abin da ya kamata su yi game da nauyin da Allah Ya dora musu na zaben shugabanni nagari masu kishin kasa da al’umma.
Ya kamata mu sani ko mu tuna, cewa a halin yanzu muna da kasa da wata shida a nan gaba domin tunkarar zaben 2015. Idan ba mu ji tsoron Allah muka yi abin da ya kamata na zaben nagartattun shugabanni a 2015 ba, wallahi ina tabbatar muku (Allah Ya kiyaye) cewa abin da muke ji ko gani a yau na bala’i da talauci da zubar da jinni da cin hanci da rashawa da sokonci da rashin iya shugabanci da raba kan ’yan kasa da sunan addini ko kabilanci da sauransu, zai zama wasan yara. Kuma ba zubar da hawaye ba wallahi idan ba mu yi hankali ba har kukan jini sai mun yi.
Gashi nan dai ya bayyana a fili, duk abin da muke gaya wa mutane ya fito fili karara. Kowa na kallo da jin abin da ke gudana a wannan kasa tamu mai albarka Najeriya. Saboda haka, yanzu ya rage namu, ko dai mu sadaukar da duk abin da Allah Ya hore mana na ilimi da dukiya da karfi da lokaci da wayo da dabara da hankali da gogewa da sauransu, mu ceto kasar nan daga rugujewa, mu ceto ta daga rubabben shugabancin danniya da rashin kwarewa da Fir’aunanci da duniya ta shaida da haka, ko kuma wallahi dukkanmu sai mun yi da-na-sani.
Idan muka ci gaba da zama wawaye ko makwadaita, marasa kishin kasa da al’umma, to ya rage namu. Kuma wallahi jiki magayi ne.
Saboda haka, ’yan siyasa da sarakuna da malamai da fastoci da shugabannin addini na Musulmi da Kirista da ’yan kasuwa da shugabannin al’umma da talakawa Musulmi da Kirista da jami’an tsaro da sauransu, ku sani hakkin ceton kasar nan ya rataya a wuyanku. Ku manta da kwadayin abin duniya, ku manta da bambance-bambance, mu hadu mu yi aiki tare, domin ganin wannan kasa tamu mai albarka ta dawo yadda take a da. Mai mutunci da zaman lafiya da kwarjini a idon duniya.
Ku sani bala’i da talauci da masifa, babu ruwansu da ko kai wane ne. Babu ruwansu da kai Musulmi ne ko Kirista, babu ruwansu da yarenka, jiharka ko yankin da ka fito.
Ya ku ’yan Najeriya! Don Allah ku kalli yadda kasarmu ta zama yau, ku kalli yadda mutuncin jami’an tsaronmu ke neman zubewa. An ki a ba su kyakkyawar kular da ta dace da kayan aiki domin tunkarar matsalar rashin tsaron da ke addabar kasarmu. Ku kalli yadda rayuwar dan Adam ta zama arha a kasar nan sakamakon rashin shugabanci nagari da zai kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Shin za mu ci gaba ne da dora maslaharmu a saman maslahar al’umma baki daya? Shin me ke damunmu ne? Wadanne irin mutane ne mu ’yan Najeriya? Ta ya ya za mu yi ta cika masallatai da coci-coci kullum da sunan ibada, amma duk na neman zama na banza, saboda mun kasa hada kai mu tabbatar da shugabanci nagari a kasarmu, har an wayi gari kasarmu na neman zama abin dariya a idon duniya? Shin mun manta cewa dukkanmu za mu mutu mu bar abin da muka tara a nan duniya ne? Mun manta za mu tashi a gaban Allah gobe kiyama mu amsa tambayoyi a kan yadda muka aiwatar da rayuwarmu a duniya ne?
Ya ku ’yan Najeriya! Ku sani, lallai shekarar 2015 ita ce shekarar da za mu gane cewa shin mun yi hankali ko kuwa har yanzu muna nan gidadawa, sako-tumaki-balle jakai? Ita ce shekarar da za mu gane, shin mun koyi darasi a jikin da muke ji a wannan kasa, ko har yanzu ba mu gane komai ba? Ita ce shekarar kwatar kai, ita ce shekarar da in har ba mu samar da canji a wannan kasa ba, to, babu lokacin da za mu iya samar da shi.
Ya ku ’yan Najeriya! Sama da miliyan 170! Ya ku Musulmi! Lallai mu sani, gyaruwar al’umma ta ta’allaka ne a kan gyaruwar shugabanni, kuma lalacewar al’umma ta ta’allaka ne a kan lalacewar shugabanni. Ma’ana; a duk lokacin da shugabanni suka zama na kirki, masu kishin kasa da al’ummarsu, to ana sa ran mutane su zama na kirki. Haka duk lokacin da shugabanni suka zama na banza, tanbadaddu, to lallai mutane haka za su kasance domin a inda akuyar gaba tabsha ruwa, ta baya ma nan zata sha. Shi ya sa Musulunci ya ba da muhimmanci sosai a kan cewa lallai jama’a su yi kokarin ganin wadanda za su zaba su jagorance su, su zamo mutanen kirki ne ba ashararai ba, adilai ba azzalumai ba, yin haka zai sa zaman lafiya da ci gaba su yawaita a kasa, soyayya da kaunar juna su watsu a kasa.
Ya ku Musulmi! Hakika Annabi (SAW) ya ba da labari cewa: “Yana daga alamomin tashin Alkiyama; ya kasance ana shugabantar da mutanen banza, jahilai, wadanda ba sa neman shiriya da Littafin Allah da Sunnar ManzonSa (SAW), kuma ba sa jin nasiha, ba sa wa’aztuwa, ba sa kwatanta adalci a tsakanin ’yan kasa kuma ba sa daukar shawara.”