Hadarin jirgin kasa ya kashe mutum 24 a Indiya
A shekaranjiya Labara ne aka ruwaito cewa akalla mutane 24 ne suka rasa rayukansu sannan wasu da dama suka jikkata a Jihar Madhya Pradesh ta kasar Indiya, sakamakon hadarin jiragen kasa fasinjoji guda biyu.An dai ce jiragen sun kauce daga kan layin dogonsu ne a kokarin ketare wata gada da ke saman kogi, a inda […]
A shekaranjiya Labara ne aka ruwaito cewa akalla mutane 24 ne suka rasa rayukansu sannan wasu da dama suka jikkata a Jihar Madhya Pradesh ta kasar Indiya, sakamakon hadarin jiragen kasa fasinjoji guda biyu.
An dai ce jiragen sun kauce daga kan layin dogonsu ne a kokarin ketare wata gada da ke saman kogi, a inda igiyar ruwa ta make su.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton masu aikin ceto suna can suna kokarin ceton mutane, amma kuma ruwan sama kamar da bakin kwarya da rashin kyawun yanayi suna kawo cikas ga aikin ceton.
Jirgin dai ya hau kan wata gada da ke saman kogi a jihar Madhya Pradesh da ke tsakiyar kasar Indiya.
Masana dai na ganin yawan faruwar hadarin da wani abu da ke damun mahukuntar kasar, inda a kullum ake samun mutane akalla miliyan 23 wadanda suke zirga-zirga a kai. Kodayake, alkalunma sun nuna cewa an samu raguwar hadarurrukan a ’yan shekarun nan, inda a shekarar 1960 aka samu hadari guda 2,000, yayin da a shekarar 2013 aka samu afkuwar hadari guda 320 kacal. Kuma daya daga cikin abubuwan da suke haddasa hadarin shi ne rashin bai wa direbobi horror da yakamata.