Hadarin jirgin ruwa ya halaka mutum 40 a Jihar Neja
A ranar Juma’ar da ta gabata ce wani jirgin ruwa dauke da fasinja 100 ya kife da jama’a da suka fito daga garin Tungar Na-illo da ke Jihar Kebbi zuwa Malele da ke masarautar Borgu a Jihar Neja domin cin kasuwa.Jama’a ne suka hango jirgin yana ta tangal-tangal a kan ruwa mutanen ciki suna ta […]
A ranar Juma’ar da ta gabata ce wani jirgin ruwa dauke da fasinja 100 ya kife da jama’a da suka fito daga garin Tungar Na-illo da ke Jihar Kebbi zuwa Malele da ke masarautar Borgu a Jihar Neja domin cin kasuwa.
Jama’a ne suka hango jirgin yana ta tangal-tangal a kan ruwa mutanen ciki suna ta ihun neman ceto. Hakan ya sa gwanayen ruwa suka fada ruwan inda suka yi nasarar ceto fiye da mutum 60 daga cikinsu.
Aminiya ta samu bayanin cewa mutum 40 sun halaka a hadarin ciki har da Sarkin Tungar Na-Illo da shugaban Gandun Dajin Kainji wadanda zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a gano gawarwakinsu ba.
Malam Zakari Idris daya daga cikin wadanda suka yi ta kai-kawo don ceto mutanen, wanda dan asalin garin ne, ya shaida wa Aminiya cewa an kai mutanen da aka ceto asibitoci bayan an ba su agajin farko. Ya ce kuma an yi wa gawarwakin da aka gano jana’iza bisa tafarkin addinin Musulunci.
Malam Zakari ya ce aukuwar lamarin ya jefa yankin cikin juyayin da za a dade ba a farfado daga gare shi ba, idan aka yi la’akari da gudunmawar da kasuwar ke bayarwa a fannin tattalin arzikin yankin.
Gwamnan Jihar Neja Dokta Mu’azu Babangida Aliyu ya ce aukuwar lamarin babbar koma baya ne ga tattalin arzikin yankin da Jihar Neja da makwabtanta da ke amfana daga dimbin alherin da ake samu a kasuwar.
Dokta Mu’azu Babangida Aliyu ya shawarci masu sufurin jirgin ruwa su rika daukar matakan kare kai ta amfani da rigar kariya ga kowane fasinja, ya ce hakan zai rage asarar rayukan da ake yi. Sannan ya nemi direbobin jiragen su rika bin ka’idar yawan fasinjojin da ya kamata kowane jirgi ya dauka a kowane lokaci.