Hadarin kwale-kwale ya ci ’yan mata 10 a Kano
Wasu ’yan mata 10 sun rasu, yayin da ake ci gaba da neman karin wasu biyu, bayan da wani kwale-kwale ya kife da su a kogin Lanjan da ke karamar Hukumar Garun Malam da ke Jihar Kano. Wani Darakta a Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kano (SEMA) Alhaji Abdullahi Aminu, ya shaida wa gidan rediyon […]
Wasu ’yan mata 10 sun rasu, yayin da ake ci gaba da neman karin wasu biyu, bayan da wani kwale-kwale ya kife da su a kogin Lanjan da ke karamar Hukumar Garun Malam da ke Jihar Kano.
Wani Darakta a Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kano (SEMA) Alhaji Abdullahi Aminu, ya shaida wa gidan rediyon BBC cewa matukin jirgin ne kawai ya tsira a lokacin da kwale-kwalen ya kife.
Daraktan ya ce jami’an hukumar sun je yankin domin ba da dukkan taimakon da ya kamata, saboda har yanzu akwai mutum biyu da ba a gano ba a cikin kogin.
Rahotanni sun ce hadarin ya auku ne sakamakon ruwan sama da ya haddasa cikowar kogin.
Rahotanni sun ce matukin jirgin ya yi ninkaya inda ya tserar da kansa, amma bai iya kubutar da ko daya daga cikin ’yan matan ba a kogi da ke toroko.
Ana danganta hadarin jiragen ruwa a kasar nan ne da dora wa jiragen fasinja da kaya fiye da kima da raunin harkar kula da gyaran jirage da kuma rashin ingantattun fitilu.