Hadarin masallaci: Har yanzu Saudiyya ba ta biya diyya ba – Hukumar Alhazai
Dokta Saleh Okenwa shi ne kwamishina mai kula da tsare-tsare da nazari da kuma yada labarai a Hukumar Alhazai ta kasa. Aminiya ta zanta da shi don jin inda aka kwana a game da alkawarin da kasar Saudiyya ta yi na biyan diyya ga mahajjata da suka rasa ransu a lokacin da gugar gini da […]

Dokta Saleh Okenwa shi ne kwamishina mai kula da tsare-tsare da nazari da kuma yada labarai a Hukumar Alhazai ta kasa. Aminiya ta zanta da shi don jin inda aka kwana a game da alkawarin da kasar Saudiyya ta yi na biyan diyya ga mahajjata da suka rasa ransu a lokacin da gugar gini da ake amfani da shi wajen fadada masallacin harami ta rikito a kansu:
Aminiya: Za mu so mu ji sunanka da kuma matsayinka a hukumar alhazai?
Dokta Saleh Okenwa: Sunana Dokta Saleh Okenwa, ni ne kwamishina mai kula da sha’anin tsare-tsare da nazari da kuma yada labarai a hukumar alhazai ta kasa.
Aminiya: Mene ne cikakken adadin mahajjatan Najeriya da su ka rasu a yayin aikin hajji da ya gabata?
Dokta Saleh Okenwa: Rasa mahajjata da Najeriya ta yi ya auku a lokaci biyu ne, na farko akwai na harami da ya auku a sakamakon rikitowar gugar gina, inda muka rasa maniyyata shida daga cikin daukacin mutane 107 da su ka rasu a wannan musabbabi, sai kuma mahajjatanmu 3 da suka tsira da raunuka. A hadari na biyu kuma wanda ya auku a kan hanyar dawowa daga Arfa, mun rasa mahajjata 274.
Aminiya: Bayan aukuwar hadari na farko, gwamnatin kasar Saudiyya ta yi alkawarin biyan diyya ga iyalan mamatan, ko wannan diyyar ya hada har da wadanda su ka rasu a wajen dawowa daga Arfa?
Dokta Saleh Okenwa: Wadanda suka rasu a wajen dawowa daga Arfa ba sa ciki, kamar yadda ka sani, bayan aukuwar na farkon, Sarkin Saudiyya bisa radin kansa ya dauki alkawarin biyan diyya na Riyal miliyan guda ga iyalan kowane mamaci, sai kuma Riyal miliyan hamsin ga wanda ya kubuta da rauni. Bayan wannan sanarwar mun aika da dukkan bayanan da ake bukata a a game da wadanda lamarin ya shafa na mahajjatanmu ga hukumomin kasar, wanda ya kunshi nau’uka biyu, wato na mamata 6 da kuma wadanda suka yi rauni mutum uku. Sannan bayan wadansu ’yan kwanaki sai suka shirya wata tawaga da ta kunshi ministan lafiya da wadansu manyan jami’an gwamnatin kasar suka kawo mana ziyara ta duba wadanda suka samu rauni, inda muka sada su da su. Sai dai a zahiri mun san hakikanin manufar ziyarar, wadda ita ce ta tantace adadin jama’ar da muka sanar da su. Sannan gabanin dawowarmu mun tattara fasfuna na mamata da kuma masu raunuka wanda ya kunshi wadansu lambobinsu, sannan na mika su ga mataimakin jakadan Najeriya a kasar, wato Counsel General, wanda dama shi ke kula da sha’anin hajji, na ce ya rika bibiyan al’amarin, saboda har lokacin dawowarmu babu wani abu da suka yi na ba da diyya.
Hukumar Saudiyya ta yi alkawari, kuma na tabbata alkawarin da ta yi ya rage bacin rai a cikin al’umma a lokacin, sai dai kash! kasa da mako biyu bayan aukuwar lamarin sai ga wata musiba da ta dara ta farko ta sake aukuwa, inda aka rasa dimbin rayuka. Na tabbata hakan ya raunana masu gwiwa, duk da cewa ba za su sauya alkawarin da suka yi da farko ba. A saboda haka har yanzu muna zaman dako ne, mu dai mun yi duk abind a ake bukata mu yi na ba su jimla da bayanai da kuma takardun shaida na wadanda lamarin ya shafa, wanda ya kunshi fasfunansu. Sai dai bayan wani lokaci da sanarwar tasu, wadansu mahajjata sun zo mana daya bayan daya a matsayin wadanda suka samu raunuka, amma kasancewar mun riga mun tattara bayani tare da mika shi, sannan har jami’ansu suka biyo baya don tantacewa, mun yanke shawarar mu tsaya a adadi na farko da muka mika, saboda zai kasance wauta mu sake zuwa ga hukumar Saudiyya dauke da wani sabon adadi na wadanda su ka yi rauni.
Aminiya: A fahimtarka me kake jin ya sa hukumar Saudiyya ta yi alkawarin biyan diyya ga wadanda hadarin harami ya shafa ba tare da sanya na hadarin da ya auku na bayan Arfa ba?
Dokta Saleh Okenwa: Kodayake wannan tambaya ga hukumomin Saudiyya ya kamata a mika ta, amma dai tun da fahimtata ka nema, to ni ina ganin sawun giwa ne ya take na rakumi. Saboda adadin wadanda suka rasu a na biyun ya dara dubu idan aka tattara na mahajjatan kasashen da lamarin ya shafa, shi ko na farko mutum dari da bakwai ne. Sai kuma abu na biyu, shi na farko a iya cewa sakaci ne na masu aikin kwangilar ginin fadada harami, wanda gwamnati za ta iya fuskantarsu a kan mai ya sa ba ku yi kaza da kaza ba, sabanin na biyu wanda turmutsutsi ne da aka yi masa fassara a matsayin wata musiba da ba a iya kauda ta, kuma a zahirin gaskiya lamarin ya faru ne a sakamakon bijirewar wasu na kin bin ka’idar da aka tsara ga masu wucewa.