Hadarin mota ya ci dogaran Sarkin Lafiya biyar
Wasu ma’aikatan fadar Mai martaba Sarkin Lafiya Alhaji Isah Mustapha Agwai su biyar sun rasu sakamakon wani mummunan hadarin mota da ya rutsa da su a garin Tilden Fulani da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi, lokacin da Sarkin da ayarinsa ke tafiya Bauchi don ta’aziyya ga Gwamnan Jihar Malam Isah Yuguda game da […]
Wasu ma’aikatan fadar Mai martaba Sarkin Lafiya Alhaji Isah Mustapha Agwai su biyar sun rasu sakamakon wani mummunan hadarin mota da ya rutsa da su a garin Tilden Fulani da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi, lokacin da Sarkin da ayarinsa ke tafiya Bauchi don ta’aziyya ga Gwamnan Jihar Malam Isah Yuguda game da rasuwar mahaifiyarsa.
A wata sanarwa dauke da sanya hannun Jami’in Watsa Labaran Fadar, Alhaji Baba Sule ta ce hudu daga cikinsu sun rasu ne a hadarin nan take inda cikon na biyar mai suna Abubakar Ibrahim mai daukar hoton fadar ya cika daga baya.
A cewar sanarwar wadanda suka rasu a hadarin sun hada da Gambo Isah Maikifi da Sallaman Sarki, Sani Inuwa da Madakin Dogarai Muhammed Umaru da Abubakar Ibrahim mai daukar hoto da kuma Muhammed Yakubu wanda shi ne direban motar.
A halin da ake ciki jama’a da dama a ciki da wajen jihar suna ci gaba da kwararowa fadar don ta’aziyya ga Mai martaba Sarkin da masarautar Lafiya dangane da aukuwar lamarin. Cikin wadanda suka kai wa Sarkin ziyarar ta’aziyya har da Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura wanda a jawabinsa a fadar ya bukaci al’umma su gudanar da rayuwa abin koyi, a cewarsa babu mahalukin da ya san ranar da zai koma ga mahallicinsa. Ya yi addu’ar Allah Ya jikan dogaran inda ya yi fata Sarkin da iyalan mamatan za su jure wannan rashi su kuma dauki lamarin a matsayin ikon Allah.
Da yake maida jawabi, Alhaji Isah Mustapha Agwai ya gode wa Gwamnan dangane da ta’aziyya ga masarautar a wannan lokaci na juyayi inda ya bayyana mamatan a matsayin masu ladabi da biyayya a koyaushe. Ya ce Masarautar Lafiya ba za ta manta da gagarumin gudunmawar da suka ba ta ba lokacin da suke raye.
Tuni aka yi jana’izarsu a Lafiya kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.