Hadarin mota ya ci masu zuwa Maulidin Nyass 40 a Jihar Bauchi
Wani hadarin tirela da ya auku a kauyen Zalau da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi dauke da wadanda suka dawo daga mauludin Sheikh Ibtahim Nyass da aka yi a Gombe ranar Asabar da ta gabata, ya ci rayukan kusan mutum 40, yayin da kusan mutum 80 ke jinya a wasu asibitocin Jihar Bauchi […]
Wani hadarin tirela da ya auku a kauyen Zalau da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi dauke da wadanda suka dawo daga mauludin Sheikh Ibtahim Nyass da aka yi a Gombe ranar Asabar da ta gabata, ya ci rayukan kusan mutum 40, yayin da kusan mutum 80 ke jinya a wasu asibitocin Jihar Bauchi da Kaduna.
Mutanen wadanda suka fito daga karamar Hukumar Soba ta Jihar Kaduna sun gamu da ajalinsu ne a yayin da suka yi wa motar cikar balbela kuma suna isowa kwanar Zalau cikin gudu sai kan ya rabu da bodinta inda ta kife da mutanen.
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa a nan take an kwashi gawarwakin mutum 40 daga baya wasu suka sake rasuwa a asibitocin da aka kai su.
Babban jami’in duba ababen hawa na karamar Hukumar Toro Yusuf Mahmud ya shaida wa wakilinmu wanda ya ziyarci yankin cewa tun daga ranar Laraba mutane suka rika zuwa Gombe don halartar Maulidin, kuma wasu daga cikin direbobin sun rika tukin ganganci, inda motoci uku ke jeruwa suna gudu kan kwalta ba tare da tunanin wasu na amfani da hanyar ba.
Ya ce a ranar Juma’a lokacin da mutanen suke wucewa da yawa an yi kusan awa uku ba tare da samun hanya ba, saboda a kiyasta sama da motoci dubu biyar masu zuwa Mauludin ne suka wuce ta yankin Toro.
Malam Yusuf Mahmud ya tabbatar da aukuwar hadarin motoci tara da suka hada da bectra hudu da bas daya da J5 daya da Opel biyu da kuma tirelar da ta jawo mutuwa mutum 38 a garin Zalau. Yayin da wasu kuma suka rasu a asibiti inda jimlarsu ta kai mutum 47.