Hadarin mota ya ci matasa hudu da ke samun horon aikin dan sanda
Matasa hudu ake sa kammala samun horo a aikin dan sanda a karshen wannan wata na Satumba sun rasu a wani hadarin mota da ya rutsa da a ranar Litinin da ta gabata a shataletalen da ke Unguwar Rogo a birnin Sakkwato. Mutum biyu daga cikinsu sun rasu ne a nan take, yayin da biyu […]

Matasa hudu ake sa kammala samun horo a aikin dan sanda a karshen wannan wata na Satumba sun rasu a wani hadarin mota da ya rutsa da a ranar Litinin da ta gabata a shataletalen da ke Unguwar Rogo a birnin Sakkwato.
Mutum biyu daga cikinsu sun rasu ne a nan take, yayin da biyu suka cika a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman danfodiyo da ke Sakkwato.
Wani da hadarin ya auku a kan idonsa, ya ce lamarin ya auku ne saboda tukin ganganci da direban motar ke yi, bayan ya dauko matasan da ake horarwa a aikin dan sanda, wadanda suka fito daga wurin koyon harbi a wani kauye a karamar Hukumar Kware zai mayar da su sansanin horarwa na jami’an da ke Unguwar Farfaru.
Ya ce matasan wadanda suke cike da murna da farin ciki da shewa a cikin babbar motar ’yan sandan da ke bude wadda suka cika ta sosai, gudun da direban ke yi ne ya sanya ta kwace masa ya watsar da su a shataletalen inda motar ta fadi rigingine.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Sakkwato, Malam Abdulkadir Muhammad da mukarrabansa sun kai ziyara asibitin da Asibitin kwararru na Jiha da na kashi da ke garin Wamakko domin duba wadanda suka samu rauni da matakin da za a iya dauka don kula da lafiyarsu. Kuma Aminiya ta iske iyalai da masu tausaya wa wadanda abin ya faru a asibitocin.
Kakakin Rundunar ta Jihar, ASP Alhaji Ibrahim ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an yi jana’izar marigayan kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada a ranar Talata, yayin da wadanda suka samu rauni suke jinya a asibitoci daban-daban.