Hadarin mota ya ci mutum 16 a Yobe

Wani hadarin mota da aka yi a gab da kauyen Dogon Kuka a karamar Hukumar Fune a Jihar Yobe ya ci rayukan mutum 16 tare da jikkata kusan 35 sakamakon taho-mu-gama da aka yi tsakanin wata motar safa samfurin Lakziriyos mai lamba MUS 760 dY da tirela mai lamba SKY 275 dB. Wani mazaunin kauyen […]

Hadarin mota ya ci mutum 16 a Yobe
Hadarin mota ya ci mutum 16 a Yobe

Wani hadarin mota da aka yi a gab da kauyen Dogon Kuka a karamar Hukumar Fune a Jihar Yobe ya ci rayukan mutum 16 tare da jikkata kusan 35 sakamakon taho-mu-gama da aka yi tsakanin wata motar safa samfurin Lakziriyos mai lamba MUS 760 dY da tirela mai lamba SKY 275 dB.

Wani mazaunin kauyen Dogon Kuka, Malam Yakubu Dogon Kuka ya shaida wa Aminiya cewa hadarin ya faru ne da misalin karfe 3:45 na yamma a ranar Litinin lokacin da tayar safar ta fashe ta kwace daga direbanta ta yi kan tirelar suka hadu.
Malamin ya ce, sun kai dauki ga mutanen da hadari ya rutsa da su inda suka rika fito da gawarwakin mutum 16 da wadanda suka samu rauni 35, kuma ba tare da bata lokaci ba aka dauke su zuwa babban asibitin Damagum.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta kasa (FRSC) a Jihar Yobe Alhaji Yusuf
Garba ya tabbatar da faruwar hadarin da mutuwar mutum 16, sai 35 sukam samu rauni daga cikin mutum 65 da ke cikin motocin biyu.