Hadarin mota ya ci mutum 55 a Yobe
Wasu munanan hadarurrukan mota biyu da aka yi a Jihar Yobe su yin sanadiyyar rasa rayukan mutum 55 inda mutum 19 suka kone kurmus. Hatdari na farko ya faru ne a ranar Lahadi a tsakanin Gashuwa da Garin Alkali inda jim kadan da tashin wata kanta dauke da wadanda suka ci kasuwar Garin Alkali ta […]
Wasu munanan hadarurrukan mota biyu da aka yi a Jihar Yobe su yin sanadiyyar rasa rayukan mutum 55 inda mutum 19 suka kone kurmus.
Hatdari na farko ya faru ne a ranar Lahadi a tsakanin Gashuwa da Garin Alkali inda jim kadan da tashin wata kanta dauke da wadanda suka ci kasuwar Garin Alkali ta auka wa wata tirela sama da mutum 20 suka rasu kuma 16 daga cikinsu ’yan mata ne.
Hadari na biyu kuma mafi muni ya faru ne a tsakanin wata bas kirar Toyota Homa mai daukar mutum 19 dauke da tambarin SURE-P da mambobin cocin Redeem da suka dawo daga Legas ta kara da wata bas kirar Golf 5 dauke da mata ’yan biki su 18.
Wata majiya a kauyen Bununu a hanyar Damaturu zuwa Potiskum inda hadarin ya faru ta shaida wa Aminiya cewa direban Toyota SURE-P din ne yana cikin gudu sai tayarsa ta fashe sai motar ta yi taho-mu gama da motar Golf 5 din, nan take Toyotar ta kama wuta, a yayin da hakan ta faru ne sai direban wata mota kirar Golf 3 ya tsorata ya kada motarsa ya shiga daji.
Wani mazaunin kauyen Malam Umaru ya shaida wa Aminiya cewa su da sojojin JTF da jami’an Hukumar Kiyaye Hadurra (FRSC) sun yi iya kokarinsu don ceto mutanen da ke cin wuta amma duka kofofin Toyotar suka ki buduwa har mutanen suka kone.
Kakakin Hukumar FRSC a Jihar Yobe, Malam Yusuf Sani ya tabbatar da faruwar hadurran biyu inda ya gargadi direbobi su daina gudun ganganci da wuce kima a yayin da suke tuki.