Hadarin mota ya ci mutum 7 ’yan gida daya

Wani hadarin mota da ya auku da motar Gombe Line a ranar Juma’ar da ta gabata a hanyar Maiduguri ya ci rayukan mutum 17 cikinsu har da mutum bakwai ’yan gida daya a Gombe.Iyalan na Malam Malami Tela da ke Jekadafari a garin Gombe hedkawatar Jihar Gombe sun rasu ne a hadarin day a auku […]

Hadarin mota ya ci mutum 7 ’yan gida daya
Hadarin mota ya ci mutum 7 ’yan gida daya

Wani hadarin mota da ya auku da motar Gombe Line a ranar Juma’ar da ta gabata a hanyar Maiduguri ya ci rayukan mutum 17 cikinsu har da mutum bakwai ’yan gida daya a Gombe.
Iyalan na Malam Malami Tela da ke Jekadafari a garin Gombe hedkawatar Jihar Gombe sun rasu ne a hadarin day a auku a tsakanin motar Gombe Line mallakar kamfanin sufuri na Jihar Gombe da tirelar kamfanin Dangote inda suka yi taho mu gama nan take fasinjojin motar Gombe Line din 17 suka kone kurmus.
Aminiya ta ziyarci gidan marigayi Malam Malami Tela inda ta zanta da babban dansa Malam Musthapha Malami wanda ya shaida wa wakilinmu cewa rashin mahaifinsu da mahaifiyarsu ya jijjiga su. Ya ce shi yana zaune a Damaturu sai kanensa ya bugo masa waya ya ce mahaifinsu sun yi hadari a lokacin da suke tafiya Maiduguri tare da mahaifiyarsu da kannensa da kuma ’ya’yan kannensa biyu.
Malam Musthapha Malami, ya ce kafin rasuwar mahaifansu sun yi waya a lokacin da suka baro Gombe inda ya tambaye su ko suna ina sai ya ce masa sun wuce Kukareta sai ya ce Allah Ya sauke su lafiya. “Gama wayarmu bai wuce minti 30 ba sai kanena ya bugo min waya ya gaya min aukuwar hadarin, kuma ba a iya gane gawarwakinsu ba saboda konewar da suka yi,” inji shi.
 Ya ce wadanda hadarin ya ci ba a iya yi musu sutura daban-daban ba saboda konewar da suka yi sai hada su mutanen garin Benishak suka yi suka yi musu sutura gaba daya aka binne su a rami daya.
 Malami Tela ya rasu yana da kimanin shekara 89 inji dan.
Muhammad Malami Rawana wanda dan marigayin ne, ya ce mahaifi da mahaifiya da ’ya’yansa biyu Aliyu da Fatima da ’yar yayarsa mai suna Ummi Muhammad duk sun rasu a hadarin. Muhammad Rawana, ya ce ba ya gari iyayensa suka yi tafiyar, amma shi ya turo musu kudin mota domin tafiya Maiduguri, sai dai a lokacin da suka isa Damaturu dansa Aliyu mai shekara bakwai ya yi masa filashin da wayar abokan tafiyarsu sai ya kira ya ce masa Abba yanzu muna Damaturu, sai ya ce musu Allah Ya kiyaye, kuma ya yi magana da kanwarsa Fatima, ya ce musu shi ma yana zuwa tare da mahaifiyasu karshen maganarsu ke nan.
Muhammad Rawana, ya ce ya kadu sosai kan rashin iyayensa da ’ya’ya biyu da ’yan uwa inda ya ce ba a taba yin irin wannan rashi a Gombe ba a ce gida daya an rasa mutum bakwai a lokaci guda.
Ya yi addu’ar Allah Ya karbi shahadarsu, saboda duk wanda ya rasu a hadarin wuta ana kyautata tsammanin ya yi shahada.