Hadarin mota ya ci ran mutum 7 a Jigawa

Wani mummunan hadarin mota ya rutsa da wadansu ’yan siyasa daga Karamar Hukumar Gwiwa a Jihar Jigawa lokacin da suke komawa gida daga Gumel, bayan  zaben fid-da-gwani na kujerar Sanatan Jigawa ta Arewa maso Gabas. Mutanen bakwai wadanda dukansu suka hallaka a nan take, an ce hadarin ya faru ne sakamakon mugun gudu da direbobin […]

Hadarin mota ya ci ran mutum 7 a Jigawa

Jami’an Hukumar Kiyaye Hatsarin Mota a bakin aiki

Wani mummunan hadarin mota ya rutsa da wadansu ’yan siyasa daga Karamar Hukumar Gwiwa a Jihar Jigawa lokacin da suke komawa gida daga Gumel, bayan  zaben fid-da-gwani na kujerar Sanatan Jigawa ta Arewa maso Gabas.

Mutanen bakwai wadanda dukansu suka hallaka a nan take, an ce hadarin ya faru ne sakamakon mugun gudu da direbobin motocin biyu suke yi. A yayin wannan tsere ne mota ta kwace wa direban da ke gaba, inda motar ta hantsula, kuma babu wanda ya fito daga motar.

Kakakin Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Bello Muhammed Zaki ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa tuni aka yi jana’izarsu kamar yadda Musulunci ya tanada. Ya ce gwamnatin jihar tana mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan wadanda suka rasa ’yan uwansu.

A gefe daya kuma Shugaban Kwamitin zaben dan takarar Sanatan Jigawa ta Arewa, a Jam’iyyar APC, Malam Ibrahim Turaki ya ce mazabar mai kananan hukumomi 12 sun kada wa Sanata Danladi Sankara kuri’u masu yawa, inda ya zama zakara da kuri’a  2,664, ya doke Sanata mai ci, Sanata Abdullahi wanda ya samu kuri’u 325.