Hadarin mota ya ci rayukan mutum 18 a hanyar Kachiya

Wani mummunan hadarin mota ya ci rayukan mutum 18 tare da jikkata wasu da dama bayan wasu motocin fasinja biyu kirar Sharon suka yi taho-mu -gama a makon jiya, inda nan take daya daga cikin motocin ta kama da wuta. Hadarin, wanda ya faru a kan hanyar Kachiya zuwa Marabar Walijo da ke karamar Hukumar […]

Hadarin mota ya ci rayukan mutum 18 a hanyar Kachiya

Wani mummunan hadarin mota ya ci rayukan mutum 18 tare da jikkata wasu da dama bayan wasu motocin fasinja biyu kirar Sharon suka yi taho-mu -gama a makon jiya, inda nan take daya daga cikin motocin ta kama da wuta.

Hadarin, wanda ya faru a kan hanyar Kachiya zuwa Marabar Walijo da ke karamar Hukumar Kachiya da ke cikin Jihar Kaduna, ya faru ne yayin da daya daga cikin motocin ta yi kokarin wuce wata tirela a daidai wani kauye mai suna Damarga, al’amarin da ya janyo motoci biyun suka yi taho-mu-gama da wacce ta fito ta daya hannun, kamar yadda wani da aka yi abin a kan idonsa mai suna Muhammadu Sani ya shaida wa Aminiya.

Ganau din ya shaida cewa bugawarsu ke da wuya sai daya daga ciki ta kama da wuta, inda duk mutanen da ke cikinta suka kone kurmus, in ban da wata mata da ta tsira da mummunar kuna a jikinta. “Ko kafin mutane su kawo dauki motar ta kama da wuta, inda aka yi cirko-cirko aka rasa ta ina za a fara, al’amarin da ya sa mutanen da ke ciki tun suna ihun neman taimako har suka gaji suka kone. Sai dai kana tsaye kawai ka yi ta jin bindiga suna fashewa, abin da matukar ban tausayi. Sai bayan da wutar ta dan lafa ne aka ga daya daga cikin fasinjojin, wata mata a gefe tana motsi. To, bayan ita dukkanin fasinjoji goma sha hudu da ke cikin motar sun mutu,” in ji shi.

“Ita kuwa da ba ta ci wuta ba, a take dai mun ga an fito da gawarwakin mutum hudu yayin da sauran kuma suka ji munanan raunuka wasu sun karairaye. Nan dai hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) suka garzaya da su asibiti, ba mu san ko wasu sun rasu daga baya ba,” inji majiyar.