Hadarin mota ya ci ’yan uwa takwas da ke dawowa daga bikin aure

Wadansu ’yan uwa takwas da suka je bikin aure a Jihar Kano daga garin Karu a yankin Birnin Tarayya Abuja, sun rasu a hadarin mota da ya rutsa da su a kusa da Gadar Malam Mamman da ke hanyar Kaduna zuwa Abuja, yayin da mutum shida suka tsira da raunuka. A zantawarta da Aminiya mahaifiyar […]

Hadarin mota ya ci ’yan uwa takwas da ke dawowa daga bikin aure
Hadarin mota ya ci ’yan uwa takwas da ke dawowa daga bikin aure

Wadansu ’yan uwa takwas da suka je bikin aure a Jihar Kano daga garin Karu a yankin Birnin Tarayya Abuja, sun rasu a hadarin mota da ya rutsa da su a kusa da Gadar Malam Mamman da ke hanyar Kaduna zuwa Abuja, yayin da mutum shida suka tsira da raunuka.
A zantawarta da Aminiya mahaifiyar mutum hudu daga cikin mamatan mai suna Hajara Haruna ta ce, baya ga ’ya’ya hudu da ta rasa a hadarin, ta rasa jikoki 2, sai kuma surukinta mai suna Alhaji Abdullahi Adamu wanda ya rasu tare da daya daga cikin dan kishiyar ’yarta.
’Yarta mai suna Sadiyya Haruna wadda ta samu raunuka da karaya a kafa, ta ce sun je bikin ’yar baffansu ne a kauyen Dimkaba’awa da ke karamar Hukumar kiru a Jihar Kano a ranar Lahadn makon jiya, sannan suka baro garin a ranar Litinin din nan, sai tayar baya ta fice daga jikin motar, al’amarin da ya sabbaba hadarin.
Ta ce sauran wadanda suka rasu kanne da yayyenta ne da kuma ’ya’yan ’yan uwa, sai kuma mijinta da kuma abokiyar zamanta mai suna Barira.