Hadarin mota ya hallaka mutum 18 a Bauchi
A ranar Lahadin da ta gabata ce hadarin mota ya ci mutum 18 sakamakon taho-mu-gama a tsakanin wata tirela da bas a kusa da kauyen Buzaye da ke kan hanyar Bauchi zuwa Jos a karamar Hukumar Bauchi da ke Jihar Bauchi.Mummunan hadarin mota wanda ya faru da misalin karfe 11:00 na dare ya auku ne […]
A ranar Lahadin da ta gabata ce hadarin mota ya ci mutum 18 sakamakon taho-mu-gama a tsakanin wata tirela da bas a kusa da kauyen Buzaye da ke kan hanyar Bauchi zuwa Jos a karamar Hukumar Bauchi da ke Jihar Bauchi.
Mummunan hadarin mota wanda ya faru da misalin karfe 11:00 na dare ya auku ne a tsakanin tirelar mai lamba dC 675 BAU da Toyota bas kirar Hiace mai lamba BAU 148 dR kamar yadda ’yan sanda suka bayyana.
Wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi (DSP) Haruna Muhammed ya fitar ta bayyana cewa tirelar wadda ta nufi Jos ta kara gaba-da gaba da bas din ce wadda ta fito Abuja cike da mutane.
“Sakamakon karawar sai bas din ta kama da wuta. ’Yan sanda masu sintiri da suke babban ofishinsu na GRA da ’yan kwana-kwana daga Kwalejin Kimiyya ra kere-kere ta Abubakar Tatari Ali da ke Bauchi sun ruga zuwa inda hadarin ya auku inda suka kashe wutar tare da daukar wadanda hadarin ya rutsa da su zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi.
Sanarwar ta ce mutum 17 daga cikin 18 din sun kone kurmus yadda ba za a iya gane su ba, yayin mutum guda tsira daga wutar amma ya rasu.
An gano cewa Alhaji Adamu Maijama’a mai kimanin shekara 45 shi ne direban motar kuma yana zaune ne a Unguwar Jahun da ke cikin garin Bauchi, yayin da fasinjan da ya tsira daga wutar mai suna Yahaya Umar mai shekara 41 yake zaune a Unguwar Dawaki a cikin garin Bauchi.
A sakon da ya aike ga iyalan mamatan Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Mohammed Abdullahi Abubakar ya nuna kaduwa kan aukuwar hadarin tare da addu’ar Allah Ya jikan marigayan.
Gwamna Mohammed Abdullahi wanda ya aike da sakon ta wata wasika da ya sanya wa hannu ya ce: “Ina cike da bakin ciki kan rasa mutum 18 da muka yi a hadarin mota a hanyar Bauchi zuwa Jos a jiya (ranar Lahadi) Allah Ya jikansu. Kuma ina fatan Allah Ya ba wadanda suka samu rauni sauki a cikin gaggawa.”
Gwamna Abubakar ya ce gwamnatinsu tana yin duk abin da ya wajaba wajen samar da ingantattun hanyoyi ga jama’arta, sai dai ya yi kiran cewa a daidai lokacin da ake fuskantar damina, hanyoyin sukan zamo masu santsi don haka ya bukaci direbobi su rika tuki a cikin tsanaki tare da kauce wa mummunan gudu ta yadda za a magance irin wannan babbar asara.