Hadarin mota ya kashe Mutum 12 a Sakkwato
Mutum 12 sun rasu sanadiyyar hadarin mota da ya faru a garin Kasarawa da ke Karamar Hukumar Wamakko a jihar Sakkwato. Wani ganau ya bayyanawa wakilinmu cewa, hadarin ya faru ne tsakanin motar tirela da ta dauko jakai da wasu mutane daga Karamar Hukumar Rabah duk a cikin jihar ta Sakkwato. Hadarin ya faru ne […]
Mutum 12 sun rasu sanadiyyar hadarin mota da ya faru a garin Kasarawa da ke Karamar Hukumar Wamakko a jihar Sakkwato.
Wani ganau ya bayyanawa wakilinmu cewa, hadarin ya faru ne tsakanin motar tirela da ta dauko jakai da wasu mutane daga Karamar Hukumar Rabah duk a cikin jihar ta Sakkwato. Hadarin ya faru ne a lokacin da motar tirelar ke hanyarta na zuwa jihar Neja, lokacin da motar ta kauce hanya.
A nan ta ke fasinjojin suka rasu lokacin da hadarin ya faru yayin da sauran suka samu mummunan rauni, a yanzu haka an kaisu babban asibitin koyarwa na jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato.