Mutum 14 sun mutu a hadarin mota a Jigawa
Wani mummunan hadarin motocin fasinja biyu ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 14 a hanyar Kano zuwa Gumel da ke jihar Jigawa ranar Asabar. Hadarin ya faru ne tsakanin wata motar fasinja kirar Golf 3 Wagon wadda zata wuce garin Gumel daga Kano ta kauce hanya ne bayan tayar motar ta fashe. Sai kuma daya motar […]
Wani mummunan hadarin motocin fasinja biyu ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 14 a hanyar Kano zuwa Gumel da ke jihar Jigawa ranar Asabar.
Hadarin ya faru ne tsakanin wata motar fasinja kirar Golf 3 Wagon wadda zata wuce garin Gumel daga Kano ta kauce hanya ne bayan tayar motar ta fashe. Sai kuma daya motar kirar Golf 3 Saloon da suka hadu a daidai Garin Galla a karamar Huklumar Ringim.
Duk motocin sun kama da wuta nan ta ke, fasinjoji takwas sun kone kurmus yayin da shida kuma suka mutu a babban asibitin Ringim, Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar SP Abdul Jinjiri, ne ya sanar da hakan.