Hadarin mota ya kashe mutum 1,602 a wata uku – FRSC
Hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya FRSC ta ce, kimanin mutum dubu 1,602 ne suka rasu a hadurra 2,805 a rubu’in shekara ta 2017. Shugaban Hukumar FRSC Mashal Boboye Oyeyemi ne ya bayyana hakan yayin gangamin wayar da kan direbobi wajen kiyaye sharrudan tuki a Jos babban birnin jihar Filato. A watannin Satumba da Oktoba da […]
Hatsarin mota
Hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya FRSC ta ce, kimanin mutum dubu 1,602 ne suka rasu a hadurra 2,805 a rubu’in shekara ta 2017.
Shugaban Hukumar FRSC Mashal Boboye Oyeyemi ne ya bayyana hakan yayin gangamin wayar da kan direbobi wajen kiyaye sharrudan tuki a Jos babban birnin jihar Filato.
A watannin Satumba da Oktoba da Nuwamba da Disamba na shekarar 2017 an samu adadin hadurra da ya kai 2,805 yayin da aka samu adadin wadanda suka rasu ya kai 1,602.