Hadarin mota ya kashe mutum 19 a Jigawa
Hadarin mota ya yi sanadiyyar rasuwar mutum 19 a wata mota kirar bas mai kujeru 18 a karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa a jiya Talata. Wadanda hadarin ya rutsa da su sun kone kurmus ta yadda ba a iya gane kamannin su, yayin da wasu kuma suka samu raunuka ciki har da jariri. Daya […]
Hadarin mota ya yi sanadiyyar rasuwar mutum 19 a wata mota kirar bas mai kujeru 18 a karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa a jiya Talata.
Wadanda hadarin ya rutsa da su sun kone kurmus ta yadda ba a iya gane kamannin su, yayin da wasu kuma suka samu raunuka ciki har da jariri.
Daya daga cikin wanda take motar ta yasar da jaririnta lokacin da hadarin ya faru.
Wani ganau ya ce, motar da ta yi hadarin mai lamba KTG245YG ta taso ne daga garin Katagun a jihar Bauchi zuwa garin Ningi.
Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Jigawa Abdu Jinjiri ya tabbatar da aukuwar hadarin.