Hadarin mota ya kashe mutum 2 da kone wasu a Bauchi
Rahotanni na bayyana cewa, wasu mutum biyu sun mutu bayan mummunan hadarin da motar su ta yi suka kone kurmus a jihar Bauchi. A cewar hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya Federal Road Safety Corps (FRSC) ta ce, hadarin ya faru ne a hanyar Bauchi zuwa Jos a yau Talata. Jami`in hulda da jama’a na hukumar […]
Rahotanni na bayyana cewa, wasu mutum biyu sun mutu bayan mummunan hadarin da motar su ta yi suka kone kurmus a jihar Bauchi.
A cewar hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya Federal Road Safety Corps (FRSC) ta ce, hadarin ya faru ne a hanyar Bauchi zuwa Jos a yau Talata.
Jami`in hulda da jama’a na hukumar kiyaye hadura FRSC shiyyar Bauchi Rilwanu Suleiman, ya ce hadarin ya auku ne tsakanin mota kirar Toyota Hilux mai lambar gwamnati da wata tankar mai da kuma wasu motoci biyu da suka kama da wuta.
Cikakken rahoton na nan tafe.