Hadarin mota ya kashe mutum 4 da raunata 4 a hanyar Legas zuwa Ibadan

Rahotanni na bayyana cewa mutum hudu aka tabbatar sun mutu yayin da wasu hudu suka samu raunuka a shataletalen garin Ogere da ke hanyar Legas zuwa Ibadan cikin jihar Ogun a yau Alhamis. Kakakin jami’an da ke lura da ababen hawa (TRACE) Mista Babatunde Akinbiyi ne ya sanarwa Kamfanin Dillancin Labarai NAN hakan yau Alhamis […]

Hadarin mota ya kashe mutum 4 da raunata 4 a hanyar Legas zuwa Ibadan

Rahotanni na bayyana cewa mutum hudu aka tabbatar sun mutu yayin da wasu hudu suka samu raunuka a shataletalen garin Ogere da ke hanyar Legas zuwa Ibadan cikin jihar Ogun a yau Alhamis.

Kakakin jami’an da ke lura da ababen hawa (TRACE) Mista Babatunde Akinbiyi ne ya sanarwa Kamfanin Dillancin Labarai NAN hakan yau Alhamis a Abeokuta babban birnin jihar Ogun.

Babatunde, ya ce hadarin ya auku ne da misalin karfe 4:30 na asubahin yau tsakanin wata babbar mota kirar Man Diesel mai lamba TKP 653 XA wanda ta dauko doya. Sannan hadarin ya jikkata mutum 14.