Hadarin mota ya kashe mutum 53 a Ghana

Kimanin mutane 53 ne suka rasa rayukansu bayan wata mota kirar bas ta yi taho-mu-gama da wata babbar mota a wani gari mai nisan Kilomita 420 daga birnin Accra na kasar Ghana, kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana.Hakazalika, wasu mutane 23 sun jikkata a hadarin na ranar Laraba da daddare, wanda kuma aka kwashe shekaru […]

Hadarin mota ya kashe mutum 53 a Ghana
Hadarin mota ya kashe mutum 53 a Ghana

Kimanin mutane 53 ne suka rasa rayukansu bayan wata mota kirar bas ta yi taho-mu-gama da wata babbar mota a wani gari mai nisan Kilomita 420 daga birnin Accra na kasar Ghana, kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana.
Hakazalika, wasu mutane 23 sun jikkata a hadarin na ranar Laraba da daddare, wanda kuma aka kwashe shekaru ba a ga irinsa ba a kasar.
Shugaban kasar  John Dramani Mahama, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka mutu a shafinsa na Twitter, kamar yadda BBC ya bayyana.
Kwamishinan ‘yan sandan yankin Brong Ahafo, Madwel Tindani ya shaida wa gidan rediyon Joy FM cewa, motar bas din ta samu matsalar birki ne, amma kuma sai direban ya debi fasinjoji ba tare da an gyara ba.
Kuma motar na kan hanyarta ne ta zuwa birnin Tamale lokacin da ta kara wa babbar motar da ke makare da kwandunan tumatur.
Tuni dai jami’an ‘yan sanda da sojoji suka isa inda lamarin ya faru, domin aikin ceto. Kuma hukumomin kasar sun ce sun fara bincike kan makasudin faruwar al’amarin.