Hadarin mota ya kashe mutum 6 a Ogun

Hadarin mota ya yi sanadiyyar rasuwar mutum shida a wani mummunan hadari da ya faru tsakanin wata babbar mota da wasu motoci biyu kirar bas a yankin J4 Ogbere a hanyar Shagamu zuwa Benin. Babbar motar dai ta kauce wa hanyar da take bi ne wanda hakan ya yi sanadiyyar hadarin. Kakakin hukumar bayar da […]

Hadarin mota ya kashe mutum 6 a Ogun

Hadarin mota ya yi sanadiyyar rasuwar mutum shida a wani mummunan hadari da ya faru tsakanin wata babbar mota da wasu motoci biyu kirar bas a yankin J4 Ogbere a hanyar Shagamu zuwa Benin.

Babbar motar dai ta kauce wa hanyar da take bi ne wanda hakan ya yi sanadiyyar hadarin.

Kakakin hukumar bayar da agajin motoci a yankin Babatunde Akinbiyi ya tabbatar da aukuwar lamarin.