Hadarin mota ya kashe mutum 7 a Yobe

Rahotanni na cewa, mutum bakwai ne aka tabbatar da rasuwarsu da mutum 10 wanda suka samu mummunan rauni a wani hadarin da motar fasinja mai kujeru 18, da ta dauko fasinjoji daga jihar Gombe zuwa Damaturu babban birnin jihar Yobe. Hadarin ya faru ne a hanyar Damaturu zuwa karamar Hukumar Potiskum a jihar Yobe. Kwamandan […]

Hadarin mota ya kashe mutum 7 a Yobe

Jami’an Hukumar Kiyaye Hatsarin Mota a bakin aiki

Rahotanni na cewa, mutum bakwai ne aka tabbatar da rasuwarsu da mutum 10 wanda suka samu mummunan rauni a wani hadarin da motar fasinja mai kujeru 18, da ta dauko fasinjoji daga jihar Gombe zuwa Damaturu babban birnin jihar Yobe.

Hadarin ya faru ne a hanyar Damaturu zuwa karamar Hukumar Potiskum a jihar Yobe.

Kwamandan Hukumar kare hadurra na jihar FRSC Mohammad Sani Hamzat ya tabbatar da aukuwar hadarin.