Hadarin mota ya kashe mutum 7 da raunata wasu a Gada-Biyu
Rahotanni na bayyana cewa, mutum bakwai sun rasu yayin da biyar suka samu mummunan rauni a wani hadarin mota da ya faru a yammacin ranar Lahadi a kauyen Gada-Biyu da ke hanyar Abuja zuwa Lokoja. Wani ganau ya shaidawa majiyarmu cewa, hadarin ya rutsa da motoci uku da wata mota kirar Toyota hayas da ya […]
Rahotanni na bayyana cewa, mutum bakwai sun rasu yayin da biyar suka samu mummunan rauni a wani hadarin mota da ya faru a yammacin ranar Lahadi a kauyen Gada-Biyu da ke hanyar Abuja zuwa Lokoja.
Wani ganau ya shaidawa majiyarmu cewa, hadarin ya rutsa da motoci uku da wata mota kirar Toyota hayas da ya faru misalin karfe 5:23 na yamma, lokacin da wata tirela kirar Daf ta tawo a guje ta afka kan motocin.
Kwamandan Hukumar kiyaye hadurra (FRSC) na shiyyar Abaji a Abuja ACC Olasupo Esuruoso ya tabbatar da aukuwar hadarin kuma ya ce, hadarin yana da nasaba ne da yawan gudu da motocin ke yi a hanyar.