Hadarin mota ya lakume mutum goma a Ebonyi
Mutane goma ne ciki har da wata mata da ’ya’yanta biyu suka mutu a wani hadarin mota da ya auku a kan titin Afikpo zuwa Abakaliki da ke cikin Jihar Ebonyi.Hadarin ya auku ne a daidai mahadar da ke kusa da tashar mota, inda ba da jimawa ba aka dauki wadanda suka samu raunuka zuwa […]
Mutane goma ne ciki har da wata mata da ’ya’yanta biyu suka mutu a wani hadarin mota da ya auku a kan titin Afikpo zuwa Abakaliki da ke cikin Jihar Ebonyi.
Hadarin ya auku ne a daidai mahadar da ke kusa da tashar mota, inda ba da jimawa ba aka dauki wadanda suka samu raunuka zuwa asibitin Abakaliki domin ba su magani, a yayin da gawarwakin wadanda suka mutu kuma aka ajiye su a dakin ajiye gawa na asibitin.
Yadda abin ya faru, kamar yadda shaidun gani da ido suka tabbatar, wata motar bas ce mai daukar mutum 18, wacce mallakin karamar Humukar Ezza ta kudu ce kuma mai dauke da lamba Ebonyi NKE 28LG, ta kai wa wata babar mnota karo, motar tana dauke da lamba DKA 17YE.
Wani da ya gane wa idonsa yadda hadarin ya faru, Mista Fabour John, ya ce ana yin yawan hadari a wannan mahadar hanya. Ya ce ba tsananin gudu ne ya haddasa hadarin ba, amma dai laifin na direban motar bas ne, wanda ya nuna gajen hakuri. Saboda haka ya yi kira ga gwamnati da ta sanya madangalai a kan daidai mahadar hanyar, domin dakatar da motoci, wanda zai rage ko ya yi maganin afkuwar hadurra a wurin.
Wani shaidar gani da idon, mai suna bictor Ituma cewa ya yi: “Hadarin ya faru ne a daidai lokacin da nake fitowa daga gidana. Ita babbar motar tana kokarin juyawa ne a lokacin da shi mai motar bas ya dake shi. Abin da ya ba ni haushi shi ne, me ya sanya babbar mota kamar wannan amma a ce a nan dan tsukukun wurin da ke da yawan hada-hada za ta juya? Lallai ya kamata a rika sanya dan sanda mai bayar da hannu a wannan mahadar hanya.”
A yayin da yake daukar mataki dangane da afkuwar hadarin kuwa, Shugaban karamar hukumar Ezza ta kudu, Joseph Egede ya rufe ma’aikatar da ke kula da motocin haya mallakar karamar hukumar, inda ya kara da cewa ba za a ci gaba da gudanar da aiki ba har sai an shirya wa direbobin kwas na musamman domin sanin makamar aiki.
“Haka kuma za a shirya masu gwaji kuma duk direban da bai nakalci tuki ya ci wannan gwaji ba zai rasa aikinsa. Ba mun ba direba mota da nufin ya kashe mutane ba ne.” Inji shi.