Hadarin mota ya raunata ‘yan sanda 3 da wasu 16

Hadarin mota ya jikkata ‘yan sanda uku da wasu fararan hula 16, wanda ya faru  a hanyar Abuja zuwa Lokoja. Wani ganau ya ce, hadarin na farko ya faru ne da ‘yan sandan da misalin karfe 11 na safe yayin da wata motar bas kirar Sienna mai lamba SMK 486 EX ta kauce hanya a […]

Hadarin mota ya raunata ‘yan sanda 3 da wasu 16

Hadarin mota ya jikkata ‘yan sanda uku da wasu fararan hula 16, wanda ya faru  a hanyar Abuja zuwa Lokoja. Wani ganau ya ce, hadarin na farko ya faru ne da ‘yan sandan da misalin karfe 11 na safe yayin da wata motar bas kirar Sienna mai lamba SMK 486 EX ta kauce hanya a kauyen Chikara.

Wanda yaga aukuwar hadarin ya ce, jami’an ‘yan sandan sun samu munanan rauni yayin hadarin, ‘yan sanda ofishin Chikara ne suka kai wadanda suka ji raunin zuwa asibitin Abaji.

Hadari na biyu da ya faru shi ne da misalin karfe 4 a kauyen Awawa inda mutum tara suka jikkata.