Hadarin mota ya rutsa da jami’an tsaro a Jigawa
Wani mummunan hadarin mota ya rutsa da jami’an tsaro masu sintiri da ake wa lkkabi Operation Salama da ke kula da shiyyar Kazaure a cikin Jihar Jigawa. Hadarin ya faru ne a a ranar Litinin da ta gabata, a misalin karfe hudu na yamma; a lokacin da jami’an tsaron suka canji abokan aikinsu na can […]
Wani mummunan hadarin mota ya rutsa da jami’an tsaro masu sintiri da ake wa lkkabi Operation Salama da ke kula da shiyyar Kazaure a cikin Jihar Jigawa.
Hadarin ya faru ne a a ranar Litinin da ta gabata, a misalin karfe hudu na yamma; a lokacin da jami’an tsaron suka canji abokan aikinsu na can Kazaure suna kan hanyarsu ta komawa daga Dutse. Suna tsakiyar gudu a daf da kauyan Caicai na karamar Hukumar Ringim, ba su ankara ba sai wani mutum ya shiga gabansu da babur. Sakamakon haka suka buge shi, wanda shi nan take ya mutu. Su kuma motar ta wuntsila da su. Nan take soja daya ya mutu kuma jami’ai 4 suka samu mugayen raunuka.
Kamar yadda bayanai suka nuna, wadanda suka samu raunin, ’yan sandan mobayil hudu, an kwantar da uku a asibiti a Dutse, domin ceton ransu, a yayin da daya jami’in soja aka kai shi asibitin Malam Aminu Kano.
Jami’in hulda da jama’a na ’yan sandan Jihar Jigawa, DSP Audu Jinjiri ya tabbatar da faruwar hadarin. Ya kara da cewa, jami’in da ya rasu yana da Mukamin Sitaf-Sajen, mai mai suna Bawa Tanko. Ya ce suna kan bincike a kan lamarin, domin sanin gaskiyar abin da ya haddasa hadarin.