Hadarin tanka ya ci mutum shida a Marabar Jos

Mutum shida ne suka halaka a wani hadarin tankar mai da aka yi a ranar Asabar da ta gaba a Marabar Jos da ke karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna. A cewar shaidu hadarin ya auku ne a lokacin da wata babbar mota ta kara da tankar man fetur da ke kokarin juyawa a gefen […]

Hadarin tanka ya ci mutum shida a Marabar Jos
Hadarin tanka ya ci mutum shida a Marabar Jos

Mutum shida ne suka halaka a wani hadarin tankar mai da aka yi a ranar Asabar da ta gaba a Marabar Jos da ke karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna. A cewar shaidu hadarin ya auku ne a lokacin da wata babbar mota ta kara da tankar man fetur da ke kokarin juyawa a gefen hanya. Hadarin ya yi matukar tada hankalin mazauna kauyen saboda wutar da ta tashi a sanadinsa. Wakilinmu wanda ya ziyarci kauyen ya ruwaito cewa akwai shagunan sayar da abinci da suka kone sakamakon kamawa da wuta da tankokin suka yi. Hadarin ya janyo cinkosan ababen hawa a kan titin Kaduna zuwa Zariya. Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya ziyarci inda hadarin inda aka yi jana’izar mamatan tare da shi. Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadari ta Jihar, Olumike Olagunju ya ce hadarin ya rutsa da mutum 10 inda mutum shida suka kone kurmus, daya daga ya samu rauni, uku kuma suka sallake rijiya da baya.Ya ce hukumarsa ta tura jami’anta zuwa wurin cikin lokaci amma ba su yi nasarar ceto mamatan ba, saboda wutar da ke ci ganga-ganga, har sai da jami’an kashe gobara ta jihar suka karaso wajen domin kashe wutar.