Hadarin tankar mai ya ci mutum 70 a Anacha

Wata tankara mai da ta kife a garin Anacha da ke Jihar Anambra ta yi sanadiyyar hallakar mutum 70 tare da raunata da dama da kuma asarar dukiya ta miliyoyin Naira. Hukumomi a jihar sun ce mutum 70 sun mutu a lokacin da tankar ta kife a wata tashar mota da ke birnin Anacha.Lamarin ya […]

Hadarin tankar mai ya ci mutum 70 a Anacha
Hadarin tankar mai ya ci mutum 70 a Anacha

Wata tankara mai da ta kife a garin Anacha da ke Jihar Anambra ta yi sanadiyyar hallakar mutum 70 tare da raunata da dama da kuma asarar dukiya ta miliyoyin Naira.

Hukumomi a jihar sun ce mutum 70 sun mutu a lokacin da tankar ta kife a wata tashar mota da ke birnin Anacha.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata, inda mutum 69 suka kone kurmus a lokacin da tankar ta kwace wa direbanta a yayin da ya shawo wata gangara, kuma wasu motocin 12 su ma suka kone.
Wasu daga cikin wadanda suka tsira da ransu suna jinya a asibiti sakamakon kunar da suka yi.
Hadarin ya yi muni sosai inda mutane a yankin suka shiga cikin damuwa a yayin da wasu rahotanni suka ce Gwamnan Jihar Anambra Mista Willie Obiano, ya barke da kuka a lokacin da ya ziyarci wurin saboda yadda ya ga gawarwakin mutane a kone.
Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kai ziyarar ta’aziyya da jaje ga muntanen jihar kan wannan bala’i da ya same su.