Hadarin tankar mai ya hallaka mutum 60 a Kuros Riba
Sama da mutum 60 ne aka kiyasta sun halaka a yayin da suke dibar ganimar man fetur a wani hadari da wata tanka mai ta yi a marararrabar Odukpani, da ke babbar hanyar Ikom zuwa Kalaba a ranar Juma’ar da ta gabata. Lamarin ya faru ne yayin da tankar man ke kokarin kauce wa ramukan […]
Sama da mutum 60 ne aka kiyasta sun halaka a yayin da suke dibar ganimar man fetur a wani hadari da wata tanka mai ta yi a marararrabar Odukpani, da ke babbar hanyar Ikom zuwa Kalaba a ranar Juma’ar da ta gabata.
Lamarin ya faru ne yayin da tankar man ke kokarin kauce wa ramukan da suke kan hanyar, sai nauyin man fetur din ya rinjayi motar, inda ta fadi gefen hanya.
Wani da hadarin ya faru kan idanunsa, mai suna Benson Bassey, ya bayyana wa wakilinmu cewa “Tankar ta yi kokarin kauce wa ramukan da ke kan hanyar ce sai man da ke cikinta ya rinjaye ta ta fadi kwanciyar magirbi.”
Ya ce “Lokacin da motar ta tadi, na ga mutane akalla 60 ko 70 dauke da galan-galan da jarkoki suna kwasar man da ke kwarara a kan titi kafin ta kama da wuta. Duk da cewa ’yan sanda sun rika korarsu, amma hakan bai sa sun tafi ba, sai ma kara yawa suke yi, ana cikin haka ne sai wuta ta kama, inda ta hallaka sama da mutum 60 wadanda idona ya iya gani.”
Wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kuros Riba, DSP Irene Ugbo game da lamarin, sai ta ce “Hakika an yi wancan hadari, amma ’yan sandan da ke gundumar Odukpani sun yi bakin kokarinsu don hana mutane zuwa dibar fetur din, amma sun ki da gobarar ta tashi ne mutanen suka gamu da ajalinsu.”